Kashe-kashen Filato: Kungiyar Arewa ta tsakiya ta sha alwashin kare kai daga Makiyaya masu kisa
- Kungiyoyin matasa a yankin arewa ta tsakiya na Najeriya sun ce ba su da wani zabi illa su fara kare kansu daga yanzu
- Yan bindiga sun mamaye yankin inda suke kai farmaki ga garuruwan yankin lokaci-lokaci
- Kungiyoyin sun ce gwamnati ta gaza kare su, saboda haka akwai bukatar su kare kansu daga maharan
Jos - Wata kungiya mai suna Save Middle Belt Nigeria ta yi Allah wadai da kisan da makiyaya ke yi wa wasu mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a yankin arewa maso tsakiya, inda suka sha alwashin cewa za su fara aikin kare kansu daga yanzu.
Kungiyar ta yi zargin cewa kashe -kashen wani bangare ne na manyan tsare-tsare da makiyayan ke yi don halaka yan asalin yankin da kuma son mallake kasar kakanninsu.
Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyara Fadar Shehun Borno, Ya Yi Magana Kan Mayakan Boko Haram Dake Mika Wuya
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran kungiyar na kasa, Philip Jwan ya sanya wa hannu, kuma jaridar Vanguard ta wallafa.
Kungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su kawo karshen kisan gillar da 'yan bindigar suke yi wa 'yan asalin Filato.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sun kuma yi kira da a gaggauta yin bitar babban tsarin rundunar sojin kasar don magance rikicin.
Wani ɓangare na jawabin na cewa:
“Daga yanzu, ba za mu ƙara nade hannayenmu muna kallon waɗannan yan ta’addan da yan bindiga suna cimma burinsu na kisan kiyashi ba.
“Kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya ba da damar kare kai. Kare kai hakki ne na kundin tsarin mulki.
"Don haka muna neman a gaggauta yin bitar babban rundunar sojojin kasar da kayan aikin leken asiri don magance wadannan munanan lamari da ke barazana ga kafuwar kasarmu."
Wasu 'yan Najeriya sun mayar da martani kan matakin matasan arewa ta tsakiya.
Umerie Chibuike Victor ya rubuta a shafin Facebook cewa:
“Ku kashe duk wanda ya zo ya kawo muku hari, wannan gwamnatin ba a shirye take ta magance matsalar rashin tsaro ba. Wannan abun bakin ciki ne.”
Satison Kaura ya rubuta:
“Wannan ita ce hanya mafi kyau ku kare kanku tunda gwamnati ta gaza. kar ku saurari alkawuran wofi daga gwamnatin Najeriya.”
Ugwuoke Henry ya rubuta:
“Babu sauran mafita 'yan'uwa. Akwai bukatar ku tashi tsaye ku kare kanku.”
Kashe-kashe: Ku kare kanku, majalisar Filato ta bukaci mazauna jihar
A baya majalisar dokokin jihar Filato ta nemi mazauna yankin da su kare kansu. Jihar ta fada cikin rikici a 'yan makonni biyu da suka gabata.
Da yake yiwa manema labarai jawabi a Jos, babban birnin jihar Filato, a ranar Juma’a, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Dasun Philip Peter, ya ce tsarin tsaro na yau da kullun ba zai iya ba da tabbacin tsaro ba.
Ya kuma ba Gwamna Simon Lalong makonni biyu ya yi aiki da kudurorin da ta gabatar masa kan yadda za a maido da zaman lafiya.
Asali: Legit.ng