Da Dumi-Dumi: Sabuwar Kungiyar Yan Bindiga Ta Bulla a Yankin Kudu Maso Gabas

Da Dumi-Dumi: Sabuwar Kungiyar Yan Bindiga Ta Bulla a Yankin Kudu Maso Gabas

  • Sabuwar kungiyar yan tada kayar baya ta bulla a jihar Imo, yankin kudu maso gabashin Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar mai suna Biafran Motherland Warrior ta fi ESN/IPOB hatsari
  • Mayakan kungiyar sun fara kai hari ga jami'an tsaro a yankin Mbaise, jihar Imo

Imo - Wata sabuwar ƙungiyar yan bindiga mai suna 'Biafran Motherland Warrior’, ta bayyana a yankin kudu maso gabashin Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa sabuwar ƙungiyar ta fi sojin ESN na haramtacciyar ƙungiyar yan aware IPOB hatsari.

A yanzun sabuwar kungiyar BMW ta fara kai hare-haren ta a yankin Mbaise dake jihar Imo, kudu maso gabashin Najeriya.

Wata kungiyaar yan tada kayar baya ta bayyana a Imo
Da Dumi-Dumi: Sabuwar Kungiyar Yan Bindiga Ta Bulla a Yankin Kudu Maso Gabas Hoto: channesltv.com
Asali: UGC

Wani sabon bidiyo da ya mamaye kafafen sada zumunta, ya nuna yadda mayakan kungiyar suke kai hari kan jami'an tsaro a Mbaise.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar goyon bayan Osinbajo ta fara kamfen na kasa baki daya, ta ziyarci Gwamna Masari na Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin jami'an tsaro na da masaniya kan kungiyar?

Wakilin dailytrust ya gano cewa mutanen dake yankin sun sanar da ayyukan da sabuwar kungiyar ke aiwatarwa a yankin.

Duk da cewa ba komai ne ya fito fili game da su, amma rahoto ya tabbatar da cewa mayakan kungiyar sun maida hankali ne wajen kaiwa jami'an tsaro hari.

Duk kokarin da akai na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Imo, ASP Mike Abattam, ya ci tura domin yaki ɗaga kiran wayar da akai masa.

A wani labarin na daban kuma kunji cewa Mutum biyu sun mutu, yayin da Sojoji suka ragargaji Yan bindiga suka kubutar da matafiya a Kaduna

Dakarun soji na Operation Safe Haven sun sami nasarar kuɓutar da wasu matafiya uku da motar su daga hannun yan bindiga.

Kara karanta wannan

Sabuwar Ƙungiyar APC Ta Buƙaci Buhari Ya Zaɓi Magajinsa Daga Kudu Maso Gabas

Rahoto ya nuna cewa maharan sun yi kokarin sace matafiyan ne a kan hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo.

Hakanan wasu yan bindiga sun hallaka mutum biyu a wani hari da suka kai kauyen Makoro Iri, jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262