Boko Haram: Amurka ta fadi dalilin da yasa Najeriya ba za ta zama kamar Afghanistan ba

Boko Haram: Amurka ta fadi dalilin da yasa Najeriya ba za ta zama kamar Afghanistan ba

  • Kasar Amurka ta ba Najeriya tabbacin zaman lafiya ba kamar yadda ya faru a Afghanistan ba
  • Amurka ta ce, lamarin Najeriya ba daidai yake da abin da ya faru da kasar Afghanistan a baya ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu ke ganin Boko Haram za su iya kwace iko a Najeriya kamar yadda Taliban ta yi

Abuja - Kasar Amurka ta ba Najeriya tabbacin cewa maimaita abin da ya faru a Afganistan ba zai taba faru ba a Najeriya dake Afrika ta yamma, The Punch ta ruwaito.

Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard ce ta bayar da wannan tabbacin ranar Litinin 30 ga watan Agusta yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Jakadiyar ta yi bayanin cewa yanayin Najeriya da Afghanistan ba daya bane.

Kara karanta wannan

Amurka ta shirya bada gudumuwa domin tona asirin wadanda ke taimakawa Boko Haram

Boko Haram: Dalilin da yasa Najeriya ba za ta zama kamar Afghanistan ba in ji Amurka
Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard | Hoto: punchng.com
Asali: Getty Images

Wasu 'yan Najeriya sun gargadi Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) kan yiwuwar abin da ya faru a Afghanistan, inda 'yan Taliban suka mamaye kasar ya faru a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun bayyana fargabar cewa halin da ake ciki a Afganistan na iya zama abin karfafa gwiwa ga Boko Haram a Najeriya wajen yunkurin mamaye kasar.

Amurka ta fice daga Afghanistan bayan shekaru 20

Bayan sama da shekaru 20 Amurka ta sanar da ficewar dakarunta na karshe daga Afghanistan jiya Litinin, inda kungiyar Taliban ta kwace iko a kasar.

Dakarun Amurka sun jagoranci rundunar kawancen tsaro ta NATO wajen fatattakar Taliban daga madafun iko a shekarar 2001 bayan harin 11 ga Satumbar 2001 da Al-Qaeda ta kai a Amurka, Kungiyar da ke da tushe a Afghanistan da kariyar Taliban.

Najeriya na da kawance mai karfi da kasar Amurka

Kara karanta wannan

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

Leonard ta lura cewa Najeriya ta kulla kawance mai karfi da Amurka, tana mai cewa yanayin ba daya bane da na Afghanistan.

Yayin da take kawar da fargabar cewa kawancen Amurka da Najeriya zai iya zama kamar na Afghanistan, ta kara da cewa:

“Ina jin mutane suna buga misali da Afghanistan sosai, ba daidai bane.
"Idan kuka saurari abin da Shugaba Biden ya fadi kan yadda sojoji suka tafi Afghanistan tun farko, saboda sun kasance cikin mummunan bala'i ne, an kashe Amurkawa sama da 3,000.
“Wannan lamarin daban ne. Kasashen da suke da dangantaka mai karfi tsakaninsu. A zahiri ba na tunanin biyun sun daidaita.”

Abin da ke faruwa a Najeriya a yau ya fara faruwa a Afghanistan a baya, in ji Omokri

Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya gargadi gwamnatin Najeriya da ta guji sake maimaita abin da ya faru kwanan nan a Afghanistan ya faru a Najeriya.

Kara karanta wannan

Rundunar soja ta karyata zarginta da ake da son maida tubabbun Boko Haram sojoji

Omokri, wanda ya roki Allah da kada ya bari Boko Haram ta kai ga kwace Najeriya; abin da Taliban ta cimma a Afghanistan, ya yi gargadin cewa kasar Afghanistan ta shaida abin da ke faruwa a Najeriya yanzu kafin daga baya ta mamaye kasar.

Amurka ta gama ficewa daga Afghanistan, jirgin karshe ya tashi ranar Litinin

A bangare guda, Hukumomin Amurka a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta sun sanar da cewa dukkan dakarunta sun fice daga kasar Afghanistan.

Jaridar Fox News ta ba da rahoton cewa jirgin C-117 na karshe dauke da membobin aiki na Amurka ya tashi daga filin jirgin saman Kabul da misalin karfe 3:29 na yamma agogon Amurka.

Fadar White House ta ce a cikin awanni 24 daga safiyar Lahadi, 29 ga Agusta zuwa Litinin, Amurka ta kwashe mutane 1,200 daga Kabul, tare da jiragen soji 26 da jiragen hadin gwiwa guda biyu dauke da wadanda suka fice daga kasar Afghanistan.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.