Amurka ta shirya bada gudumuwa domin tona asirin wadanda ke taimakawa Boko Haram

Amurka ta shirya bada gudumuwa domin tona asirin wadanda ke taimakawa Boko Haram

  • Amurka ta shirya taimaka wa Gwamnatin Tarayya a kan matsalar tsaro
  • Mary Leonard ta ce akwai maganar nemo masu daure wa Boko Haram gindi
  • Jakadar Amurka tace za su taimaka a gano masu taimaka wa ‘Yan ta’addan

Abuja – Punch ta rahoto cewa Kasar Amurka ta bayyana shirinta na tallafa wa Najeriya domin a gano wadanda suke hura wutar ta’addanci a kasar nan.

Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Leonard ta bayyana wannan a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021, yayin da ta gana da manema labarai a garin Abuja.

Amurka za ta hada-kai da Najeriya?

An tambayi jakadar ketaren ko gwamnatin Amurka ta shirya bada gudumuwa da nufin a tono wadanda ke daure wa ta’addanci gindin zama a Najeriya.

Mary Beth Leonard mai shekara 59 ta ce yanzu haka ana tattauna wa a game da wannan lamarin.

“Wannan wani abu ne da muke daukin mu hada kai da Najeriya a kai.”
“Mun yi zama sau uku, muna magana a kan wannan batu a watanni biyu da suka wuce."

Buhari, Joe Biden
Shugaban Najeriya da Joe Biden Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“Ba zan so in shiga bayani dalla-dalla ba.”

Tsoron abin da ya auku a Afghanistan

Jakadar ta kasar wajen a Najeriya ta tabo batun tsoron dangatakar Najeriya da Amurka ya zama kamar yadda lamarin ya kasance a kasar Afghanistan.

A cewarta, akwai alaka mai kyau tsakanin Amurka da Najeriya, wanda hakan ya sa dangantakar da ke tsakaninsu ya sha bam-ban da Afghanistan.

Shugaban dakarun sojojin Amurka a Turai, Janar Jeffrey Harrigian ya bayyana yadda alakar Amurka da Najeriya ta dawo bayan cinikin Super Tucano.

“Cinikin jiragen saman A -29 Super Tucano ya bamu dama mu dawo da alakar da ke tsakaninmu.”

A ranar Lahadi ne gwamnatin Jihar Kaduna ta yi karin-haske a kan kisan Kyaftin Abdulkarim Na’Allah, babban 'dan Sanatan Kebbi, Bala Na Allah.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bukaci Jami’an tsaro su gano wadanda ke da hannu a wannan mugun aiki domin a dauki mataki a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel