Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

  • Sanata Ali Ndume, ya kirayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fito ya yiwa yan Najeriya jawabi
  • Sanatan APC yace bai kamata Buhari ya yi gum da bakinsa a lokacin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara ba
  • Sai dai sanatan ba shi da shilafa cewa sojoji zasu zakulo waɗanda suka kai musu hari NDA ko ina suka ɓuya

Abuja - Shugaban kwamitin sojojin ƙasa, Sanata Ali Ndume, ya nuna matukar damuwarsa kan shirun shugaba Buhari game karuwar matsalar tsaro a faɗin kasa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar dattijai, ya roki Buhari ya daina magana ta bakin mataimakansa a kan muhimmin abu kamar tsaron kasa.

Sanatan ya yi wannan furuci ne a wata hira da yan jarida a Abuja yayin da yake tsokaci kan harin da yan bindiga suka kai NDA.

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari Hoto: @Buharisallau
Asali: Instagram

Ndume yace:

"Ina damuwa sosai da rashin jawabin shugaban ƙasa ga yan Najeriya. Shiru a halin da ake ciki ba abu ne mai kyau ba."
"Idan har shugaban Amurka zai dinga jawabi kullum saboda abinda ke faruwa a kasar Afghanistan, Zan tsammaci shugaban ƙasa zai wa yan Najeriya jawabi kullum ko mako-mako ko duk bayan mako biyu kan halin da ake ciki a faɗin kasa."
"Kalaman da mataimakan shi suke yi ba mafita bace, ya kamata shugaban kasa ya samu wani lokaci da zai rinka yiwa yan kasa bayanin halin da ake ciki da kuma matakin da gwamnati ke ɗauka."

Wane tasirin bayanin Shugaba zai wa yan Najeriya?

Ndume yace jawabin shugaban ƙasa ka iya rage radaɗin damuwa da tsoron dake cikin zukatan yan Najeriya idan suka ji matakan da ake ɗauka.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Sanatan yace ya kamata shugaban ya rinka ziyartar inda wani abu ya faru domin gane wa idonsa yanayin da ake ciki.

Ku zakulo bara gurbin cikinku

Sanata Ndume ya bayyana tabbacin cewa sojoji zasu zakulo gungun yan bindigan da suka kai hari makarantar soji NDA.

Sai dai ya roki jami'an sojojin su fallasa bara gurbin dake cikinsu, waɗanda ke baiwa yan ta'adda bayanai.

A wani labarin kuma Kotu Ta Maida Uche Secondus Mukaminsa Na Shugaban Jam'iyyar PDP

Yayin da kusoshin PDP da suka haɗa da gwamnoni da mambobin kwamitin amintattu suka amince da naɗa shugaban riko na PDP ta kasa.

Wata babbar kotu a jihar Kebbi ta soke hukuncin dakatarwa, ta maida Uche Secondus kan kujerarsa ta shugaban PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262