Babbar Magana: Ministan Buhari Ya Fallasa Yadda Ake Sata Ta Karkashin Kasa a Mulkin Shugaba Buhari
- Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yace koda ana sata a mulkin Buhari to sai dai ta karkashin kasa
- Yace amma a gwamnatin baya zaka ga mutum na wadaka da dukiya bayan ko shago ɗaya bai mallaka ba
- A cewar Amaechi, Gwamnatin Buhari tana kokarin rike amanar dukiyar kasa fiye da sauran gwamnatocin baya
Abuja - Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, yace ana sata amma sai dai a sirrince karkashin mulkin shugaba Buhari.
Amaechi yace gwamnatin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta fi kowace gwamnati kokarin kare dukiyar al'umma.
Ministan ya yi wannan furuci ne yayin da yake amsa tambayoyi a wata fira da ya yi da jaridar dailytrust.
Da aka tambayesa game da gwamnatin shugaba Buhari, Amaechi yace wannan gwamnatin ta fi kowace rike amanar dukiyar yan ƙasa idan aka kwatanta da sauran.
Shin ana satar dukiyar kasa a fili kafin yanzu?
Amaechi ya kara da cewa ba kamar a baya lokacin da zaka ga mutum ba shi da hanyar samun ko naira ɗaya amma ya zama miliyoniya.
A cewarsa kuma babu matakin da ake ɗauka kan irin waɗannan mutanen a baya, wannan ba zai taba faruwa karkashin Buhari ba.
Ministan yace:
"Ina son yan Najeriya su yi adalci, zaka iya fitowa fili ka saci kudi a wannan gwamnatin? ba wai ina maganar muna cin hanci bane ko ba mu yi."
"Mu ɗauka muna sama da faɗi da dukiyar kasa, shin zaka iya ftowa fili ka saci kuɗi a wannan gwamnatin? Amma a gwamnatin baya meke faruwa? a kan titi za'a yi sama da kuɗaɗen al'umma."
"Cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a gwamnatin baya, ta yadda bama ta tashi ake ba. Ba kunya zaka ga mutum yana wadaka da dukiyarsa a fili kowa na gani."
Ana sata a gwamnatin Buhari amma a sirrince
Amaechi ya kara da cewa a wancan lokacin ko me ka yi kuma ko nawa ka ɗiba babu wanda zai hukunta ka.
Yace:
"Zaka gansu ko shagon kafinta ba su mallaka ba amma sun zama biliyoniya, kuma ba su boye wa."
"Amma a wannan gwamnatin, idan zakai satar kuɗi, sai dai ka yi a sirrince. Ba wai ina nufin abu ne mai kyau ba, babban laifi ne da ake hukunta wanda aka kama."
"Amma a gwamnatin baya, zaka saci dukiyar yan kasa ba wanda zai ce maka uffan, in ma an kama ka ba abinda za'ai maka. Amma a mulkin Buhari, da zaran an cafke ka zaka fuskanci hukunci."
A wani labarin kuma Mutum uku sun mutu yayin da miyagun Yan bindiga suka kai sabon hari jihar Kaduna
Wasu gungun yan bindiga sun kai sabon hari kauyukan dake yankin karamar hukumar Zangon Kataf, Kudancin Kaduna.
Lamarin ya faru ne a kauyen Machun da kuma Manuka, inda akalla mutum uku suka mutu wasu suka jikkata.
Asali: Legit.ng