Ida Ba Mu Yi Dagaske Ba, Wataran Za'a Kore Mu Daga Abuja, Ministan Buhari

Ida Ba Mu Yi Dagaske Ba, Wataran Za'a Kore Mu Daga Abuja, Ministan Buhari

  • Ministan sufuri kuma tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, yace ya zama wajibi a zage dantse wajen shawo kan komai
  • Ministan yace a koda yaushe burin shugaba Buhari shine yadda za'a gina Najeriya kan tubali mai inganci da sahihanci
  • Yace yace Abuja da kowa ke guduwa yana dawowa saboda tsaro, wataran za'a kori kowa matukar ba'a ɗauki mataki ba

Abuja - Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya zargi wasu gurbatattun yan siyasa da kokarin tarwatsa albarkatun ƙasa, inda ya kara da cewa hakan yana da hatsari.

A wata hira da dailytrust, ministan yace shugaban ƙasa Buhari, yana yin iyakar abinda zai iya wajen gina ƙasar nan kan tubali mai kyau.

Tsohon gwamnan Rivers na tsawon zango biyu ya bayyana cewa karuwar matsalolin rashin tsaro ka iya shafar babban birnin kasar a kwana a tashi.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Ministan Buhari Ya Fallasa Yadda Ake Sata Ta Karkashin Kasa a Mulkin Shugaba Buhari

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi
Ida Ba Mu Yi Dagaske Ba, Wataran Za'a Kore Mu Daga Abuja, Ministan Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ministan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abinda shugaban kasa yake cewa shine, mu gina muhimman ayyuka a kasa. Shugaban ya kan tambaye mu ya zaka ji idan ka tsinci kanka a Cafe Town? Kunya zaka ji a matsayinka na ɗan Najeriya saboda wasu. gurbatattu sun kacaccala mana arzikin mu."
"Yace abu ɗaya da zaka ji ana zancen Najeriya shine ya kamata ka kai ziyara Abuja, garin ya haɗu sosai. Amma fa Abuja ba ta ɗaukar nauyin kowa, idan bamu yi dagaske ba wataran sai an kore mu daga Abuja."
"Mutum nawa ne manyan masu faɗa a ji da suka fice daga jihojinsu? Sun tsere sun dawo nan Abuja, saboda ta fi tsaro don shugaban ƙasa na ciki. Wata rana waɗannan yaran zasu sami karfin guiwa, da kafar mu zamu fice."

Wane mataki zamu bi don warware matsalolin?

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban APC, Adams Oshiomhole, Ya Fadi Abinda Zai Faru da Yan Najeriya a 2023

Amaechi ya kara da cewa matukaar ba'a dawo kan maganar shugaban ƙasa ba, a tabbatar an tattala albarkatun da Allah ya bamu.

Bugu da kari, Amaechi yace:

"Idan har bamu bi maganar shugaba Buhari ba cewa kada mu rarraba kan mu kan arzikin da Allah ya bamu kuma mu aiwatar da muhimman ayyuka, to babu bukatar zama tsinstiya ɗaya."
"Wasu na cewa masu fafutukar ɓallewa sune matsalar mu, ba haka bane; wargajewar tattalin arziki da rashin adalci sune manyan matsalolin mu."
"Shin a kan wannan gwamnatin aka fara rashin adalci? Tun baya ake haka domim ni shaida ne, to wajibi mu maida hankali wajen magance shi."

A wani labarin kuma FG Ta Fara Rabawa Talakawa Masu Karamin Karfi N20,000, Ta Bayyana Rukunin Mutanen da Zasu Amfana

Gwamnatin tarayya ta fara biyan tallafin N20,000 ga mutane 74,000 a jihar Kogi, waɗanda aka tantance karkashin shirin CCT, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

Gwamnati ta kirkiro shirin CCT (Conditional Cash Transfaer) ne domin bada tallafin N5,000 ga magidanta masu karamin karfi karkashin tsarin NSIP a ma'aikatar jin kai da walwala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel