A huɗubar Juma'a, Sheikh Nuru Khalid ya caccaki Buhari, yace ya bar ƴan bindiga suna mulki

A huɗubar Juma'a, Sheikh Nuru Khalid ya caccaki Buhari, yace ya bar ƴan bindiga suna mulki

  • Babban limamin masallacin Apo legistlative Quaters, Sheikh Nuru Khalid, ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wankin babban bargo a kan kasa kawo karshen ta’addanci a Najeriya
  • Ya bayyana takaicin da ke zuciyarsa a lokacin hudubar Juma’a, inda yace Buhari ya sami Najeriya a dunkule amma ya bar ‘yan ta’adda sun fara mulkar wani bangare daga cikin kasar
  • Ya kara da cewa duk wanda zai fada wa Buhari ya je ya fadi, ya ce karkashin mulkinsa ne kadai ake tsorata mutane ta hanyar umartarsu da su bayar da kudi ko kuma a kai musu hari

Kaduna - Babban limamin masallacin Apo Legistlative Quarters, Sheikh Nuru Khalid, ya caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kasa kawo karshen ta’addanci a kasar nan.

Yayin hudubarsa ta ranar Juma’a, Limamin ya ce Buhari ya samu Najeriya a dunkule amma ya bar ‘yan ta’adda suna mulkar wani bangare na kasar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Buhari ya tarar da Najeriya kai haɗe, ya bar ƴan bindiga suna mulkar sassan ta - Sheikh Khalid
Buhari ya tarar da Najeriya kai haɗe, ya bar ƴan bindiga suna mulkar sassan ta - Sheikh Khalid. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
Kuje ku fada wa shugaban kasa cewa a karkashin mulkinsa ne wasu bangare na jama’a suka fara bukatar mutane ba su kudade ko kuma su fuskanci farmaki,” a cewar Khalid.
Sai su tattara kudi kuma su sanar da duniya cewa a ranar Juma’a 'yan bindiga suka ce za su karba don gudun su kai farmaki.
A sanar da shugaban kasa cewa akwai kasar da muke biyan kudin zama cikinta, sannan akwai kasar da ba mu sani ba, wacce ‘yan bindiga ne suke shugabantar ta.
Ko dai shugaban kasa ya dawo da kasar nan a dunkulenta, yadda ya tarar da ita ko kuma Allah ya azabtar da shi.
Wannan sako ne. Kuma ina tura shi a ne a budaddiyar hanyar kuma ina so duniya ta ji kuma ta gani. Na yarda ni na furta duk maganganu na, kuma zan fuskanci kowanne hukunci aka yanke min saboda ina wa’azi a kan zaman lafiya da dunkulewar kasa.

Kara karanta wannan

Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

Shugaban kasa, ba ma son jin rahotanni a kan kashe-kashen da ake yi kana gani. Ba ma son mu samu rahotanni a kan matsoratan sojoji wadanda ake kai wa farmaki har sansaninsu.
Muna da bidiyon da ka ke cewa sojojin Najeriya suna da kwarewa, kwazo da dagiyar da za su kawo karshen duk wani ta’addanci a kasar nan. Ka ce da za a zabeka da tuni ka basu gudunmawar kawo karshen duk wasu ‘yan ta’adda a kasar nan.
Ka yi mana alkawari kuma ka ki cika wa. Idan ka rasa masu baka shawara gani ina tuna maka. Muna maka addu'ar Allah ya baka ikon cika wannan alkawarin in har kana da burin hakan.

Cikar Najeriya shekaru 61: FG ta kafa kwamitin mutum 12 domin shirye-shirye

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta rantsar da kwamitin mutane 12 da suka hada da ministoci domin tsara yadda shagalin bikin cika murnar shekaru 61 da samun 'yancin kan kasa.

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Najeriya za ta cika shekaru 61 a ranar 1 ga watan Oktoba.

A yayin rantsar da kwamitin a ranar Alhamis a Abuja, sakataren gwamnatin tarayya, SGF Boss Mustapha, ya ce hikimar nan ta biyo bayan bukatar fara shirin shagalin da wuri domin samun sakamako mai kyau, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel