Gidaje 5 na hafsoshin soja 'yan bindiga suka balle a NDA Kaduna
- ‘Yan bindigan da suka shiga barikin Afaka da ke NDA a jihar Kaduna ranar Talata sun afka gidaje 5 wadanda suke kusa da juna ne
- Kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatar, sun ci karensu babu babbaka ne saboda dakarun soji basu yi saurin zabura ba
- Sannan sun yi hanzarin yin ta’addancinsu cikin gaggawa sannan suka lallaba suka tsere cikin dan kankanin lokaci
Kaduna - ‘Yan bindigan da suka shiga barikin Afaka da ke NDA a jihar Kaduna ranar Talata sun fada wa gidaje 5 da ke makwabtaka da juna ne.
An samu wannan bayanin ne a wata takarda wacce Daily Trust ta gani.
Kamar yadda jami’an binciken sirri suka bayyana, ‘yan bindigan sun ci karensu babu babbaka saboda sojojin ba su yi gaggawar zabura ba a kan lokaci.
Lokaci mai tsawo da sojoji suka dauka a ranar da aka kai harin shi ya bai wa ‘yan bindigar damar balle har gidaje 5 da ke makwabtaka da juna sannan suka yi gaggawar tsere wa kafin sojojin su motsa,” kamar yadda takardar tazo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta ruwaito cewa, take a wurin suka harbe manyan sojoji har lahira sannan suka yi garkuwa da wani manjo.
Akwai wani soja da ya samu miyagun raunika, yana asibiti ana kulawa da lafiyarsa a asibiti.
Janar Lucky Irabor ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, kuma ya ce lamarin ya fi kama da hauka.
Lamarin da ya faru a Kaduna ya fi kama da fashi da makami. Abin bai yi kama da ta’addanci zalla ba,” a cewarsa.
Kada wani ya damu da matsalar rashin tsaro. Shiyasa zamu yi gaggawar ganin mun kawo karshen irin wannan haukar.”
Kano: 'Yan sanda sun damke mahaifiyar da ta garkame tare da hana dan ta abinci
A wani labari na daban, wata mata a jihar Kano ta shiga hannun 'yan sanda sakamakon kama ta da laifin garkame dan ta mai shekaru 12 da tayi tare da hana shi abinci na tsawon shekaru.
Daily Trust ta wallafa cewa, Maryam Dauda ta shiga hannun 'yan sandan jihar Kano ne bayan an kama ta laifin garkame dan ta a wani daki a gidan da suke a Unguwar Liman Dorayi dake karamar hukumar Gwale ta jihar ba tare da bashi abinci ba da kuma kula da lafiyarsa.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa har yanzu matar tana hannunsu kuma za a gurfanar da ita nan babu dadewa bayan an kammala bincike.
Asali: Legit.ng