Rashin tsaro: Mun taba yi wa mutum 76 jana’iza a lokaci guda, babu wanda ya ji labari inji Sultan
- Sarkin Musulmi ya sake koka wa kan yadda ake fama da matsalar rashin tsaro
- Muhammad Sa’ad Abubakar III yace ba zai daina fadawa gwamnati gaskiya ba
- Sultan yace a magance matsalar ba tare da an neni taimakon kasashen waje ba
Abuja - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, yace ba a bada cikakken labari a kan irin kashe-kashen da ake fama da shi a yau.
Mutane ba su sanin abubuwan da ke faruwa
Daily Trust ta rahoto Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III yana cewa sha’anin rashin tsaro ya yi kamari, ya kuma yi alkawarin cigaba da fadin gaskiya.
Da yake jawabi a wajen taron majalisar addinai na kasa a birnin tarayya Abuja, Sultan ya bada labarin wata rana da aka birne mutum 76 a garin Sokoto.
“A Sokoto kurum, akwai wata rana da muka birne mutane 76, ‘yan ta’adda suka kashe su haka kurum, mutane ba su samu labarin wannan ba.”
“Akwai kuma ranar da muka birne gawar mutane 48 a Sokoton dai, amma ba a ji labarin ba.”
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana cewa dole a bankado mutanen da suke yin wannan danyen aiki, domin a yanke masu hukuncin da ya dace.
A nemi gudumuwar kasashen waje?
Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga jami’an tsaro su nemo duk masu daukar nauyin ta’addanci, ko da kuwa shugabannin addinai ne ko jagororin wata kabila ne.
“Dole mu dage wajen kawo karshen wannan lamarin, idan mun ga dama, za mu iya tsaida shi. Idan aka gayyaci kasar waje, ba a san yadda za ta kare ba.”
“Ina wannan bayani ne daga zuciya ta saboda mun damu da yadda abubuwa suke kasance wa.”
Jaridar ta rahoto Sultan yana zargin shugabannin al’umma da ‘yan siyasa da yin kalaman kiyayya da za su iya jawo a rika kashe mutane ba da dalili ba.
“Ba za ka kashe mutum bai ji ba, bai gani ba, da sunan addini, kuma ka ce za ka tafi gidan Aljanna, kana yaudarar kanka ne, wutar jahannama za ka shiga.”
Ana cigaba da kashe-kashe a Filato
Wasu fusatattun matasa sun kai wa ‘Yan Majalisar dokoki da Gwamnan jihar Filato gawawwakin mutanen da aka kashe a sabon harin da aka kai a Yelwan Zangam.
Masu zanga-zanga sun fito da gawan wadanda aka kashe daga asibiti, sun ajiye su a kofar shiga gidan gwamna domin a shaida irin kisan gillar da aka yi wa jama'a.
Asali: Legit.ng