Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

  • Tsohon dan kwallon Akwa United, Christo Davies ya mutu sakamakon cigaba da rikicin addini da ke yi a Jos, babban birnin Jihar Plateau
  • Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan afkuwar lamarin ba, majiya daga iyalan tsohon dan wasan sun ce rikicin garin ne ya ritsa da shi
  • A baya-bayan nan, an halaka matifya su 22 da suka fada hannun wasu miyagun da suka yi musu kissar gilla

Tsohon dan wasan kwallon Nigeria wanda ya buga wasa a kungiyar Akwa United, Chris Davies ya mutu sakamakon rikicin ya ake yi a Jos, babban birnin jihar Plateau, Best Choice Sports ta ruwaito.

Majiyoyi daga iyalan marigayin suna ikirarin cewa ya mutu ne sakamakon rikicin addini da ke cigaba da ruruwa a birnin a yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos
Tsohon dan wasan Akwa UnitedChristo Davies. Hoto: Akwa Ibom Sports
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin hada wannan rahoton, babu cikakken bayani kan afkuwar lamarin amma abin damuwa ne yadda garin Jos ke fuskantar kallubalen tsaro a yan kwanakin nan.

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun harbe wasu matfiya a karamar hukumar Jos ta arewa a makon da ta gabata.

A gano cewar wadanda abin ya faru da su suna ratsawa ne ta garin na Jos yayin da suka fada hannun yan bindigan da suka bude musu wuta a motarsu.

A kalla gawar mutum 15 ne aka kai dakin ajiyar gawa na asibitin kwararru na Plateau yayin da sauran mutanen kuma ba gano inda suke ba.

Muhammad Ibrahim, daya daga cikin fasinjojin da ya tsira daga harin ya ce suna mota ne mai daukan mutum 18 yayin da yan bindigan suka bude musu wuta.

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

A wani labarin daban, kun ji cewa kungiyoyi biyu na wasu shu’uman ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda harbe-harbe ya barke tsakaninsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rikicin ya yi sanadiyyar halakar mutane 9 a cikinsu kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel