Daliban Islamiyya ta Tegina 5 na cikin mawuyacin hali – Shugaban makarantar

Daliban Islamiyya ta Tegina 5 na cikin mawuyacin hali – Shugaban makarantar

  • Biyar daga cikin yaran makarantar Islamiyya ta Tegina da ke hannun ‘yan bindiga na cikin mawuyacin hali
  • Shugaban makarantar, Abubakar Alhassan, ne ya bayyana cewa yan bindigan sun kirasa don sanar da shi halin da yaran ke ciki
  • Hakan na zuwa ne bayan mutuwar wasu shida daga cikin daliban a baya

Neja – Wadanda suka yi garkuwa da yaran makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko sun bayyana cewa biyar daga cikin yaran da ke tsare suna cikin mawuyacin hali kuma suna iya mutuwa nan ba da jimawa ba.

Shugaban makarantar, Alhassan Garba Abubakar, ya ce masu garkuwar sun fada masa haka a hirar su ta karshe.

Daliban Islamiyya ta Tegina 5 na cikin mawuyacin hali – Shugaban makarantar
Yan bindigar sun nemi a biya naira miliyan 18 bayan kudaden da aka biya a baya Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Masu garkuwa da mutanen, sun ce a shirye suke su karbi kudin fansa na farko na naira miliyan 18 domin sakin yaran ga iyayensu.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

Amma gwamnatin jihar Neja ta yi watsi da sabon ci gaban a matsayin wata dabara da masu garkuwa da mutane suka shirya don samun karin kudi daga iyayen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An bayar da rahoton cewa biyu daga cikin yaran da aka sace sun mutu a ranar Alhamis da ta gabata.

Alhassan ya ce 'yan bindigar sun yi kiran gaggawa a waya, inda suka yi ikirarin cewa ba sa son wasu yaran su mutu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya ce:

“Sun kira ni kuma sun ba da labarin mutuwar. Sun bukace ni da in gaggauta domin a saki yaran domin biyar daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
"Da mutuwar yara biyu da hudun farko da suka fara rasuwa, shida daga cikin yaran yanzu sun rasu duk da cewa mun biya Naira miliyan 50 a baya, muna addu’a a wannan karon Allah ya taɓa zuciyarsu su sake su.”

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Jaridar The Nation ta fahimci cewa iyayen sun sake fara tara kudi don hana ci gaba da mutuwar yaran su.

An tattaro cewa iyayen suna cikin damuwa game da yadda wasu daga cikin yaran ke cikin mawuyacin hali.

Amma Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Ibrahim Matane, ya shaida wa jaridar cewa 'yan fashin suna amfani da irin wannan dabarar don samun ƙarin kuɗi daga iyayen kuma a ƙarshe ba za su saki yaran ba.

Ya nemi iyayen da su kwantar da hankalinsu, yana mai ba da tabbacin gwamnati tana kan lamarin kuma za ta dawo da yaran cikin koshin lafiya.

Matane ya dage cewa matakin gwamnati na rashin biyan kudin fansa yana nan amma ya kara da cewa wannan ba yana nufin cewa gwamnati ba ta yin komai kamar yadda mutane da yawa ke gani ba.

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

A baya mun ji cewa da alamun yara shida cikin 136 na daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko Islamiyya, dake Tegina jihar Neja sun mutu hannun yan bindigan da suka sace su.

An yi garkuwa da wadannan yan ta'alikai ne ranar 30 ga Mayu a makarantarsu dake Tegina, karamar hukumar Maru ta jihar.

Ance Shugaban makarantar, Abubakar Alhassan, ne ya bayyana cewa yan bindigan sun kirasa don sanar da shi mutuwar yaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel