Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Kaduna kan raba kudin fansa, sun kashe juna har mutum 9
- Wasu yan bindiga sun rasa rayukansu yayinda suka budewa jina wuta a jihar Kaduna
- Rahoton ya nuna cewa wanna abu ya auku ne a karamar hukumar Giwa
- Majiyoyi sun bayyana cewa wannan ya auku ne sakamakon rashin jituwa kan kudin fansa
Kaduna - Akalla yan bindiga tara sun rasa rayukansu sakamakon rashin jituwa da ya auku tsakanin bangarorin tsagerun daban-daban a jihar Kaduna.
Gwamnatin jihar a ranar Juma'a ta bayyana cewa rahoton leken asiri da na jami'an tsaro sun tabbatar da hakan.
A cewar rahoton ChannelsTV, wannan rikici ya auku ne ranar Laraba a karamar hukumar Giwa ta jihar.
An ce wani shahrarren dan bindiga mai suna Godon Mota ya dira kauyen Garke tare da yaransa kuma tada hayaniya.
Duk da cewa ba'a tabbatar da takamammen abinda ya haddasa rigimar ba, majiyoyi cewa rikicin na da alaka da rabon kudin fansa.
Daya daga cikin kungiyoyin sun yi zargin cewa an cucesu wajen rabon - kuma hakan ya hadda rikicin.
Garkuwa da mutane ya zama babban masana'anta
Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a Arewa maso yammacin Najeriya da Arewa maso tsakiya.
A shekara daya yanzu, yan bindiga sun kai hari garuruwa a jihohin wadannan yankunan kuma daruruwan mutane sun rasa rayukansu.
An yi awon gaba da daliban makaranta a Kaduna, Zamfara, Katsina, Kebbi da Neja inda akalla dalibai 1000 sukayi kwanaki hannun yan bindiga.
An biya miliyoyin kudi matsayin kudin fansa don sakin wadannan dalibai.
Yaki da ta'addanci: Janar Irabor na neman taimakon hafsoshin soji da suka yi murabus
A wani labari na daban, a ranar Laraba, Shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya, Janar Leo Irabor, ya ce sojoji suna bukatar samun dabaru da kwarin guiwa daga sojojin da suka yi murabus don cigaban kasa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya yi wannan furucin ne yayin jawabi a wani taron karawa juna sani na manyan sojojin Najeriya na yankin arewa ta tsakiya da suka yi a Makurdi.
A cewarsa, sojoji suna da damar da zasu kawo karshen duk wasu rashin tsaro da suke addabar kasa, amma ya bukaci sojoji masu murabus da kada su sare ko su yi tunanin sun fita daga cikin masu baiwa kasa tsaro, hasalima su amince da cewa suna da ruwa da tsaki a harkar tsaro.
Asali: Legit.ng