Yaɗa bidiyon baɗala: Sadiya Haruna ba jarumar Kannywood bace – Alhassan Kwalli

Yaɗa bidiyon baɗala: Sadiya Haruna ba jarumar Kannywood bace – Alhassan Kwalli

  • Alhassa Kwalli, jigo a hukumar tace fina-finai ta MOPPAN ya nesanta masana'antar Kannywood da Sadiya Haruna
  • Kwalli ya bayyana cewa sabanin yadda ake yayatawa, sam Sadiya bata da nasaba da masana'antar fim din
  • Hukumar Hisbah dai ta garkame matashiyar bisa zarginta da yada badala a kafofin sada zumunta

Kano - Shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma daya daga cikin masu ruwa da tsaki a Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i (MOPPAN), Alhassan Kwalli ya yi martani a kan matsayin Sadiya Haruna a masana’antar.

Alhassan ya ce sabanin yadda ake ta yayatawa, Sadiya ba jarumar Kannywood bace domin bata daya daga cikin ‘ya’yan masana’antar.

Yaɗa bidiyoyin baɗala: Sadiya Haruna ba jaruman Kannywood bace – Alhassan Kwalli
Alhassan Kwalli ya ce sabanin yadda ake fadi, Sadiya Haruna ba 'yar Kannywood bace Hoto: @sayyada_sadiya_haruna
Asali: Instagram

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa jigon na MOPPAN ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta.

Ya kuma gargadi jaruma Ummah Shehu da ta kalmasa harshenta sannan ta wanye lafiya kamar kowani jarumi.

Ya ce:

“Muna so mu ja hankalin Ummah Shehu da ta kiyaye harshenta da kuma lafazinta, sannan ta zauna lafiya kamar kowa.
“Sannan muna kara jan hankalinta cewar wadda ta ke magana a kanta ba ‘yar Kannywood ba ce, saboda na ga kafafen yada labarai sun dauka ‘yar Kannywood ce, ba ‘yar Kannywood ba ce.
“Saboda haka don Allah don Annabi, muna kira da abokan sana’armu da su san irin kawayen da za su dinga jawo mana cikin wannan masana’anta.”

Ya kuma yi addu’ar samun rabauta daga ubangiji, da kuma addu’ar samun zaman lafiya a wasu yankuna na Najeriya da ake fama da matsalar tsaro..

Hisbah ta garkame Jarumar Kannywood kan saka al'amuran baɗala a kafar sada zumunta

A baya mun kawo cewa hukumar Hisbah ta kulle jarumar masana'antar shirya fina-finai Kannywood, Sadiya Haruna, bisa saka abubuwan baɗala a shafukanta na sada zumunta.

Dailytrust ta ruwaito cewa shugaban sashin kula na hukumar Hisbah, Malam Aliyu Usman, shine ya jagoranci damke wacca ake zargi, mazauniyar Kabuga a Kano.

Jarumar ta cigaba da zama a hannun hukumar Hisbah har zuwa ranar Litinin da safe, inda aka gurfanar da ita gaban kotun shari'ar musulunci dake zamanta a Sharada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel