Jarumi Adam Zango ya bayyana alaƙarsa da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

Jarumi Adam Zango ya bayyana alaƙarsa da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

  • Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana dalilin yanke alakarsa da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab
  • Ya wanke kansa ne tun bayan yadda cece-kuce saka yawaita a kafafen sada zumuntar zamani akan batawar su da jarumar
  • A wata hira da akayi da shi ya bayyana cewa kowa ya san shi da ita kuma ya dauke ta ne a matsayin diyar sa

Kaduna - Sanannen jarumin Kannywood, Adam Zango ya bayyana abinda ya janyo suka raba jiha da matashiyar jarumar Kannywood, Ummi Rahab.

Ya yi karin hasken ne a wata hira da BBC ta yi da shi sakamakon yadda rahotanni iri-iri suka yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani wanda ya bayyana dangantakar dake tsakaninsu duk da dai sun bata yanzu.

Jarumi Adam Zango ya bayyana alakarsa da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab
Jarumi Adam Zango ya bayyana alakarsa da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab. Hotuna daga @official_adam_zango da @official_ummi_rahab
Asali: Instagram

Tauraron ya ce surutai ne kawai na mutane inda kowa yake ta tofa albarkacin bakinsa akan abubuwan da suka hada shi da Ummi.

Ya bayyana cewa yana jinta tamkar diyarsa ne, don haka jama’a suna ta soki-burutsu ne, maganar tsuntsaye. Ya kuma bayyana yadda yake amsar kaddara a duk yadda ta zo masa a rayuwa.

Kamar yadda jarumin yace:

Kowa ya san ni da Ummi, kuma duk wanda kace ka daukeshi a matsayin da to sai dai ka yi ta masa addu’o’i. Domin ta sauya hanya ta fara bin mara kyau.

Har yanzu dai jarumar bata fadi wata magana ba dangane da kalaman Zango, sai dai BBC tana kokarin ganin ta same ta don jin ta bakinta.

A hirar ne Zango ya bayyana yadda yake kulawa da ita tun tana da shekaru 11 a duniya amma dai ba a wurinsa take ba, a hannun iyayenta take.

Kamar yadda yace:

Ina kulawa da ita a masana’antar Kannywood, ina kokarin ganin na kare mutumcin ta don daura ta a hanyar da ta dace a cikin masana’antar.

Sai dai an dakatar mata da harkar fim kafin ta girma kuma bayan ta girma shi da kan shi ya dawo da ita.

Rabuwa ta da Ummi Rahab, Adam Zango

Ya bayyana yadda suka rabu sakamakon yadda take bijire wa umarninsa tana gudanar da harkokinta yadda take so.

Kamar yadda ya shaida, ba wani abu na daban bane ya faru tsakaninsa da Ummi ba kamar yadda mutane suke ta yadawa suna juya lamarin.

Idan ka haifi yaro ba ka haifi halinsa ba ballantana wanda daukarsa ka yi a matsayin da. Idan dai zan rike yaro in ce masa ga abinda zai yi amma ya ki yi, in hana shi ya ki hanuwa, to an yi kafin ita kuma da aka zo kan ta na ce taje Allah ya bayar da sa’a, inji jarumin.

'Yan bindiga sun sace mutane 50, sun kashe wasu huɗu a Zamfara

A wani labari na daban, 'Yan bindiga sun kashe mutane hudu sun kuma yi awon gaba da wasu mutanen 50 a garin Gora Namaye da ke karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara kamar yadda yan sanda suka sanar a ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa jami'in hulda da mutane na rundunar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Litinin a Gusau.

Shehu ya ce maharan, sun zo da dimbin yawa sun kutsa garin da tsakar daren ranar Lahadi, suka kashe mutane hudu sannan suka sace mutane 50, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel