Abin da yasa ba za mu hukunta tubabbun ƴan Boko Haram ba, Gwamnatin Tarayya

Abin da yasa ba za mu hukunta tubabbun ƴan Boko Haram ba, Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce ba za ta hukunta ko halaka tubabbun yan Boko Haram ba
  • Lai Mohammed, Ministan Sadarwan Nigeria ne ya bayyana hakan a Washigton DC, Amurka
  • Ministan ya ce hukunta su bayan sun mika wuya ya saba da tsari da ka'idoji na yadda ake karbar fursunonin yaki na duniya
  • Mohammed ya ce abin da sojoji za su yi shine su tantance su don tabbatar da tubar na gaskiya ne daga bisani a mayar da su cikin al'umma

Washington DC, Amurka - Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce ba za ta hukunta tubabbun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram ba domin hakan ya saba wa nagartaccen tsari na kasashen duniya, Daily Trust ta ruwaito.

Lai Mohammed, Ministan Sadarwa na Nigeria, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar da ya yi da kafafen watsa labarai na duniya a birnin Washington DC, a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?

Abin da yasa ba za mu hukunta tubabbun ƴan Boko Haram ba, Gwamnatin Tarayya
Ministan Sadarwa da Al'adu na Nigeria, Lai Mohammed. Hoto: Daily Trust
Asali: Depositphotos

Daily Trust ta ruwaito cewa Ministan Sadarwan ya ce neman a kashe ko hukunta tubabbun yan Boko Haram a maimakon yi musu afuwa ya saba wa ka'idar tsari nagari da kasashen duniya ke kai.

Wane matakin sojojin za su dauk kan tubabbun yan Boko Haram?

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ta ruwaito Mohammed na cewa:

"Na yi magana da hukumomin sojoji da kai na kafin in baro Nigeria kuma sun ce abin da suke yi shine tsarin da duniya ta amince da shi game da sojoji da suka mika wuya don haka za a dauke su ne tamkar fursunonin yaki."
"Ba zai yi wu kawai ka bindige su ba saboda akwai yarjejeniya na kasashen duniya da ya bawa fursunonin yaki yanci suma. Abin da sojoji ke yi shine, idan sun mika wuya, za su gudanar da bincike a kansu su tabbatar tubarsu na gaskiya ne sannan daga bisani a mayar da su cikin al'umma."

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa Yan Ta'adda Ba Zasu Iya Kwace Najeriya Ba Kamar Afghanistan, Lai

A baya-bayan nan, mayakan kungiyar Boko Haram tare da iyalansu da dama suna ta mika wuya ga rundunar sojojin Nigeria.

Hakan ya janyo hankulan yan kasa inda wasu ke ganin bai dace a yafe musu ba duba da cewa sun halaka mutane farar hula a da ma sojoji a baya.

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa Wajibi Sheikh Pantami Ya Yi Allah Wadai da Abinda Taliban Ta Yi a Afghanistan, HURIWA

Asali: Legit.ng

Online view pixel