'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

  • Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun damki wani Adeyemi Tosin, ma’aikacin banki bisa zargin wawurar kudin wani abokin huldarsu dake ajiya a bankin
  • Ana zargin Tosin da kwashe naira miliyan 10 daga asusun bankin Oladele Adida Quadri mai shekaru 78 tsakanin ranar 12 ga watan Augusta da ranar 13 ga watan
  • Sakamakon bincike ya bayyana yadda Tosin ya bude wani asusu a wani banki na daban yayi ta kwasar kudaden yana zubawa a sabon asusunsa

Oyo - Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Kara karanta wannan

Sunayen Matafiya fiye da 20 da aka yi wa kisan gilla a Jos, wani ya rasa 'yanuwansa 7

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa
'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Yadda al'amarin ya kasance

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa an gano yadda matsalar ta auku bayan ATM ya hadiye katin Quadri a reshensu na Ibadan, Shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Quadri ya nemi taimakon ma’aikacin ne bayan ya shiga bankin inda ya bashi duk wasu bayanansa.

Kamar yadda Tribune Online ta wallafa, wanda ake zargin ya yi amfani da damar ya bude sabon asusu yayi ta wawurar kudaden mutumin yana zubawa a asusunsa.

Yanzu haka ana cigaba da bincike akan wadanda suke da hannu a lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ngozi Onadeko ta bukaci mutanen kirkin jihar su hada kai da ‘yan sanda wurin taimakawa a kammala binciken, a cewar Osifeso.

Kara karanta wannan

Bincike: Da gaske ne magajin Abba Kyari, Tunji Disu, sabon shugaban IRT ya isa ritaya?

Yakasai: Abin Da Yasa Na Shiga Damuwa Kan Gayyatar Da EFCC Ta Yi Wa Bukola Saraki

A wani labari daban, Alhaji Tanko Yakasai, Dattijon Dan Kasa, a ranar Litinin ya ce akwai yiwwar gayyatar da EFCC ta yi wa tsohon shugaban majalisa Bukola Saraki na da alaka da siyasa, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke magana a Kano, Yakasai ya ce akwai yiwuwar gayyatan yunkuri ne na karya wa tsohon shugaban majalisar gwiwa don kada ya yi takarar shugaban kasa a 2023 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce abin ya dame shi domin Saraki tamkar da ya ke a gare shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164