Wata sabuwa: Yadda wani gwamna ya sauya mahaifinsa, ya ce Obasanjo ne mahaifinsa

Wata sabuwa: Yadda wani gwamna ya sauya mahaifinsa, ya ce Obasanjo ne mahaifinsa

  • Gwamnan jihar Ogun ya bayyana wata magana mai nauyi ga tsohon shugaban kasar Najeriya
  • A cewar gwamnan, tunda yanzu mahaifinsa ya rasu, yanzu ba shi da baba sai dai Obasanjo
  • Ya bayyana haka ne yayin da tsohon shugaban kasar na Najeriya, Obasanjo ya je masa jaje

Ogun - A wani lamari mai ban mamaki, gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya sanar da canza sunan mahaifinsa kwanaki bayan rasuwar mahaifin nasa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kai masa ziyarar ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa.

Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Abiodun ya ce Obasanjo ya kasance mahaifinsa tsawon shekaru tun kafin ma mahaifin nasa ya kwanta-dama, ya kara da cewa dole ne tsohon shugaban ya tsaya masa a yanzu a matsayin mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Kaduna kan raba kudin fansa, sun kashe juna har mutum 9

Wata sabuwa: Wani gwamna ya sauya sunan mahaifinsa, ya ce Obasanjo ne mahaifinsa
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa:

"Baba, ba inda za ka. Baba, cikin ikon Allah, za ka kara tsawon rai. Ba za mu iya jurewa ba ka tafi yanzu. Ka kasance mahaifina tsawon shekaru, amma, yanzu mahaifina na haihuwa ya tafi ya sadu da tsarkakanasa, dole ne ka tsaya yanzu don zama mahaifina.”

Ya roki Obasanjo da ya dauki nauyinsa a matsayin mahaifinsa tunda mahaifinsa ya mutu, ya kara da cewa tunda tsohon shugaban bai yi watsi da bukatar ba, ana iya aminta da cewa ya amince da shi nan take.

Kamar yadda rahoton ya nuna, gwamnan ya samu nasarar 'shiga' ga dangin Obasanjo, daga asalin sa na Abiodun.

A martaninsa, Obasanjo ya ce mahaifin gwamnan, Pa Abiodun ya mutu cikin salama, ya kara da cewa tsawon shekara 89 na rayuwarsa, babu wanda ya taba zarginsa da aikata miyagun ayyuka.

Kara karanta wannan

Obasanjo bayan gana wa da PDP: Najeriya na iya tabarbarewa idan ba a kula ba

Ya ce rayuwa mai tsawo a irin wannan lokaci a cikin wannan yanayi na bakin ciki a cikin kasar da Allah ya ba ta kyakkyawar hula amma babu kai da zai sa ta, babban aiki ne.

Obasanjo bayan gana wa da PDP: Najeriya na iya tabarbarewa idan ba a kula ba

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis 19 ga watan Agusta ya bayyana kwarin gwiwa cewa har yanzu Najeriya za ta kai ga matsayi mafi girma kuma za ta sami matsayi mai kima a cikin hadin kan kasashen duniya.

Obasanjo ya fadi haka ne a Abeokuta yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Prince Uche Secondus, Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Punch ta ruwaito.

Obasanjo ya bayyana taron a matsayin wanda ba a tsara shi ba yana mai bayyana cewa kofofinsa za su kasance a bude ga kowa da kowa ta hanyar matsayin da ya mallaka a Najeriya.

Kara karanta wannan

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

Obasanjo: Shekaru 35 ciwon suga na azabtar dani ba kakkautawa, amma ban mutu ba

A wani labarin, Tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ba bayyana sirrin yadda ya ke lallaba rayuwarsa da ciwon suga a shekaru 35 da suka gabata, yayin da ya ce ciwon ya kashe abokan sa da dama amma shi gashi nan garau, Daily Nigerian ta ruwaito.

Cif Olusegun Obasanjo ya fede biri har wutsiya kan batun a ranar Laraba 18 ga watan Agusta a wani bikin da ya halarta na rufe taron ci gaban yara masu ciwon suga na jihar Ogun da aka gudanar a Abeokuta ta jihar ta Ogun.

Taron wanda Cibiyar Ciwon suga ta Talabi ta shirya, ya koyar da yara 21 da ke fama da ciwon suga mataki na 1 a jihar kan yadda ake fama da cutar.

A wani rahoto da Daily Trust ta rahoto, Obasanjo ya ja hankali da kuma shawartar yara da su kula da cutar suga matuka ta hanyar kiyaye salon rayuwa, yana mai cewa ciwon suga ba cuta ne da bai kai wa ga halaka.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel