Hotuna da bidiyoyin kasaitacciyar liyafar cin abinci dare ta bayan daurin auren Yusuf da Zahra

Hotuna da bidiyoyin kasaitacciyar liyafar cin abinci dare ta bayan daurin auren Yusuf da Zahra

  • Gagarumar liyafar cin abinci dare aka shirya bayan daurin auren Yusuf Buhari da amaryarsa Zahra Bayero
  • Tabbas wurin ya dauka kala ganin yadda 'ya'yan shugabanni da masu fadi a ji suka halarci wurin, har da 'yan fim
  • An ci, an sha tare da girgijewa yayin da matasa da 'yan mata suke taya masoyan murnar babbar ranarsu

Kano - Allah ya nufa, alkawarin masoya ya cika. A jiya ne Juma'a ne aka daura auren da namiji daya tilo na shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero, diya ga sarkin Bichi, Mai martaba Alhaji Nasir Ado Bayero.

Auren da minsitan sadarwa, Ali Isah Pantami ya daura kan sadaki naira dubu dari biyar a masarautar Bichi, ya kwashi shugabanni, 'yan siyasa, 'yan kasuwa na kasar nan da ketare.

Kara karanta wannan

Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa dan Shugaba Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu, an yi cece-kuce

Hotuna da bidiyoyin kasaitacciyar liyafar cin abinci dare ta bayan daurin auren Yusuf da Zahra
Hotuna da bidiyoyin kasaitacciyar liyafar cin abinci dare ta bayan daurin auren Yusuf da Zahra. Hoto daga @thebeginningofyz
Asali: Instagram

Jim kadan bayan daurin auren, jama'a sun dinga tururuwa inda suka garzaya wurin liyafar cin abincin dare da aka hada domin ango Yusuf Buhari da matarsa, Gimbiya Zahra Nasir Bayero.

Tabbas wurin ya matukar daukar kala ganin yadda 'ya'yan gwamnoni, ministoci, masu mulki, 'yan kasuwa, har da 'yan fim suka yi dafifi domin taya sabbin ma'auratan murna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotuna da bidiyoyi da shafin bikin mai suna @thebeginningofyz suka dinga wallafawa a Instagram sun nuna yadda aka ci, aka sha tare da cashewa a wurin liyafar.

An ga amarya ZZahra da nagonta Yusuf sun shiga wannan hayakin na soyayya yayin da sauti mai ratsa zuciya yake tashi, su kuwa suna takawa cike da kasaita da alfarma

Asali: Legit.ng

Online view pixel