'Yan Najeriya sun yiwa Abiola addu'a bayan hoton Alkur'ani da ya ba da gudunmawa a wani masallaci ya bayyana

'Yan Najeriya sun yiwa Abiola addu'a bayan hoton Alkur'ani da ya ba da gudunmawa a wani masallaci ya bayyana

  • Marigayi MKO Abiola ba attajirin dan kasuwa da dan siyasa bane kawai, ya kasance mai alkhairi ba tare da la’akari da addini ko kabilanci ba
  • Kwanan nan, wani dan Najeriya mai suna Abdulkarim Abu Harisah ya tsinci kwafin Alkur'ani Mai Girma wanda mai taimakon jama'an ya bayar
  • Mutane da yawa sun mayar da martani ga hoton ta hanyar yin addu’a ga wanda ake tsammanin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 1993 wanda aka soke wanda ya mutu a 1998

'Yan Najeriya a dandalin sada zumunta na Facebook sun yi addu'a ga marigayi mai taimakon al'umma kuma dan siyasa, Moshood Kashimawo Abiola, wanda aka fi sani da MKO, bayan hoton kwafin Alkur'ani da ya bayar ya bazu.

Abdulkarim Abu Harisah ne ya wallafa hoton a Facebook a ranar Talata, 3 ga watan Agusta, inda ya ce ya ga kwafin Littafin Mai Tsarki a masallacin unguwarsa.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

'Yan Najeriya sun yiwa Abiola addu'a bayan hoton Alkur'ani da ya ba da gudunmawa a wani masallaci ya bayyana
'Yan Najeriya sun yiwa Abiola addu'a bayan hoton Alkur'ani da ya ba da gudunmawa ya bayyana a yanar gizo Hoto: PIERRE BOUSSEL/AFP via Getty Images, Abdulkarim Abu Harisah via Facebook
Asali: UGC

Abu Harisah ya wallafa:

"@MKO Abiola) (rahimahullah) ... Na ga kwafin wannan Alqur'ani a masallacin unguwana. Dole sai da na bude shi da sauri na karanta wasu ayoyi domin Abiola ya sami ladan ayyukan da ya yi wa Musulunci. Allah ya karbi jarinsa da gafarta masa."

'Yan Najeriya sun yi wa MKO addu’a

Da suke mayar da martani ga wallafar Abu Harisah, 'yan Najeriya da yawa sun yi wa marigayi mai taimakon jama'a addu'a.

"WaLloohi, wannan mutumin yayi kokari sosai. ALLAH ya gafarta masa kurakuransa."

Adetayo Abdjaami'i Adenuga ya ce:

"Aameen. Allah kuma ya saka muku kuma da alheri kan fatan alkhairin da suka yi wa musulmin da ya rasu. Wasu mutane za su mai da hankali kan kurakurai sannan kuma su fara cin mutunci ko ma tsinuwa!"

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Attajirin Dan Kasuwa, Okunbo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Shugaba Buhari Ya Yi Jimami

Auwalu Aminu Hassan ya ce:

"Allah ya ba shi Aljanna."

MKO Abiola ya kasance a ofishina a lokacin yakin neman shugabancinsa na 1993, Garba Shehu

A wani labarin, hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya magantu a kan haduwarsa da marigayi MKO Abiola a shekarar 1993 kafin zaben shugaban kasa.

A wani sako da ya wallafa a shafin Facebook a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, Shehu ya ce ofishin sa a matsayin babban manajan kamfanin buge-bue na Janar Triumph shi ne wuri na farko da dan siyasar ya yada zango a lokacin da ya zo Kano don kamfen din sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel