Kwamishinar jihar Kano ta bayyana yadda tsohon malaminta na sakandare ya zama mijinta

Kwamishinar jihar Kano ta bayyana yadda tsohon malaminta na sakandare ya zama mijinta

  • Kwamishinar harkokin mata ta jihar Kano, Malama Zahra'u Umar, ta yi bayanin yadda ta hadu da mijinta
  • Zahra’u ta bayyana cewa ta auri wani mai tsoron Allah wanda ya kasance malaminta a makarantar sakandare
  • A cewarta, tana addu'ar Allah ya ba ta mutum tsayayye, mai kirki da gaskiya a matsayin abokin rayuwa

Kano, Kano - Malama Zahra’u Umar, kwamishinar harkokin mata ta jihar Kano, ta bayyana cewa mijinta abin kaunarta kuma mahaifin ‘ya’yanta ya kasance malaminta yayin da take makarantar sakandare.

A wata tattaunawa ta musamman ta wayar tarho da wakilin Legit.ng, Adewunmi Adeoye, kwamishinar ta bayyana cewa tsananin tausayin mutumin da kasancewarsa mai tsoron Allah ne ya sanya mata son shi.

Kwamishinar jihar Kano ta bayyana yadda tsohon malaminta na sakandare ya zama mijinta
Malama Zahra'u ta bayyana mijinta a matsayin mutum mai tsoron Allah Hoto: Adewunmi Adeoye.
Asali: UGC

Mijina mutum ne mai tsoron Allah

Ta ce mijinta yakan ce tana aiki da yawa kuma tana shiga cikin mutane da yawa; saboda haka, ya fada mata da ta dan huta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

“Na hadu da mijina lokacin ina makarantar sakandire kuma shi ne malamin mu. Ba zan yi ƙarya a nan ba, yana da kirki sosai kuma yana da tsoron Allah kuma waɗannan su ne halayen da nake fata a cikin mutum kuma godiya ga madaukaki saboda ya ba ni.
"A kan abin da yake so na daina, koyaushe yana ba ni shawara in ɗan huta saboda koyaushe ina aiki kuma ina hulɗa da mutane da sauran abubuwan da suka shafi aiki."

Ta bayyana cewa ana yi mata lakabi da sunan "Uwar Marayu" saboda irin tasirin da ta ke yi a rayuwar marasa galihu.

Kotu ta yankewa barawon Al-kur'ani hukucin sharan masallaci na kwanaki 30 a Kano

A wani labarin, wata kotun shari’a da ke zama a Fagge 'Yan-Alluna a Kano ranar Talata 17 ga watan Agusta ta umarci Halifa Abdullahi da ya share masallacin Juma’ar Fagge na tsawon kwanaki 30 a jere a matsayin hukuncinsa na satan kwafin Alkur’ani mai girma guda takwas.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

Mista Abdullahi, mazaunin unguwar Yola da ke cikin birnin Kano, an zarge shi da sata a masallaci a unguwar Tudun Maliki ranar Lahadi da daddare tare da kwashe kwafin Alkur'ani guda takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel