Shugaba Buhari Ya Tura Wakilai Na Musamman Zuwa Kano Domin Daura Auren Yusuf da Gimbiya Zahra
- Shugaban kasa Buhari ya aike da wakilai na musamman daga cikin kusoshin gwamnatinsa zuwa Kano
- Wakilan zasu je Kano ne domin halartar ɗaura auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero
- Za'a gudanar da ɗaura auren ne ranar Jumu'a 20 ga watan Agusta a babban masallacin Jumu'a na garin Bichi
Kano - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tura tawagar wakilai na musamman domin ɗaura auren ɗansa, Yusuf da Zahra, ɗiyar sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Tawagar wakilan, bisa jagorancin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, zata je Kano ne domin halartar ɗaura auren da aka shirya gudanarwa ranar Jumu'a.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai taken, "Tawagar shugaban ƙasa zuwa Kano domin halartar manyan taruka biyu."
Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shine ya fitar da wannan sanarwa ranar Alhamis.
Su waye wakilan da Buhari ya tura?
A cewar sanarwar, tawagar fadar shugaban ƙasan sun haɗa da ministoci kamar ministan tsaro, Bashir Salihu Magashi.
Sannan akwai ministan noma, Alhaji Sabo Nanono, Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, da kuma ministan albarkatun ruwa, Hussein Adamu.
Sai dai bayan kammala ɗaura auren, Mallam Garba Shehu zai tsaya ya wakilci shugaba Buhari a wurin taron mika sandar mulki ga sarkin Bichi.
An tsaurara tsaro a Bichi
Masarautar Bichi a jihar Ƙano ta cika da jami'an tsaro ta ko ina yayin da ake cigaba da shirye-shiryen ɗaura auren Yusuf, ɗa ɗaya tilo ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari , da amaryarsa Zahra, ɗiyar sarkin Bichi.
Shirye-shirye sun yi nisa domin ɗaura auren wanda aka tsara za'a gudanar a babban masallacin Jumu'a na Bichi da karfe 1:30 na ranar Jumu'a.
A wani labarin kuma Kanwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Rigamu Gidan Gaskiya
Yar uwar kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, wacce take binsa ta rigamu gidan gaskiya, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Marigayya mai suna, Hussaina Umaru, yar kimanin shekara 50 ra rasu ne ranar Alhamis bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng