Gwamnoni, Attajirai, da sauran manyan kasa za su je Bichi wajen auren ‘Dan Shugaban kasa

Gwamnoni, Attajirai, da sauran manyan kasa za su je Bichi wajen auren ‘Dan Shugaban kasa

  • ‘Dan shugaban kasar Najeriya zai auri ‘Diyar Sarkin Bichi a ranar Juma’ar nan
  • Yusuf Buhari zai auri Zahra Nasiru Ado Bayero a babban masallacin garin Bichi
  • Mutanen garin Bichi a jihar Kano za su ga manyan bakin da ba su taba gani ba

Bichi za ta yi manyan baki

Kano - Rahotanni sun tabbatar da cewa Garin Bichi zai yi cikar da ba a saba gani ba a karshen makon nan.

A ranar Juma’a, 20 ga watan Agusta, 2020, ‘dan shugaban Najeriya, Yusuf Muhammadu Buhari zai auri ‘diyar Sarkin Bichi, Zahra Nasiru Bayero.

Bayan wannan babban daurin aure da za ayi, gwamnatin jihar Kano za ta ba Mai martaba Nasir Ado-Bayero sanda a matsayin Sarkin garin Bichi.

Premium Times tace Nasir Bayero zai karbi sandar girma ne wata guda bayan an ba ‘danuwansa, Aminu Ado-Bayero wanda ke rike da kasar Kano.

Kara karanta wannan

An Tsaurara Tsaro a Bichi Yayin da Ake Shirye-Shiryen Bikin Yusuf Buhari da Zahra Bayero

Shugaban kwamitin shirya taron auren, Nura Shehu Ahmed, ya shaida wa manema labarai cewa shugaba Muhammadu Buhari zai halarci taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Madakin Bichi, Shehu Ahmed, ya bayyana wa ‘yan jarida a ranar Laraba, za a daura auren ne a babban masallacin Juma’a na garin.

‘Dan Shugaban kasa
Buhari ya zama surukin gidan Ado Bayero Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Bayan an daura auren da karfe 1:30 na rana, washegari kuma gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai ba mai martaba Nasir Ado-Bayero sandar-girma.

Bayan shugaban kasa da tawagarsa, ana sa ran cewa gwamnonin jihohin kasar nan daga duka jam’iyyun za su halarci wannan bikin aure da za ayi.

Kamar yadda aka ji, za a gudanar da lacca ta musamman a makarantar FCR da ke garin Bichi, bayan addu’o’i na musamman da za ayi gobe da yamma.

Yusuf Buhari zai zama Ango

Talban na Daura shi ne na uku da Muhammadu Buhari ya aurar bayan ya zama shugaban kasa. Kafin yanzu ya aurar da ‘ya ‘ya mata; Zahra da Hannan.

Kara karanta wannan

Na so diyata ta kammala karatunta kafin aure, Sarkin Bichi kan shirin auren diyarsa da Yusuf Buhari

Yusuf Buhari kadai ne ‘da namiji da shugaban Najeriya yake da shi yanzu a Duniya, kuma shi ne ‘da na biyu wajen mahafiyarsa, Aisha Muhammadu Buhari.

Babban ‘dan shugaban kasar, Musa Buhari ya rasu shekaru da-dama da suka wuce. Matar farko da Buhari ya aura, Safinatu ce ta haifa masa wannan yaro.

Yusuf Buhari: Talban Daura

Kwanaki baya ne aka ji Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk ya ba Yusuf Buhari sarautar ‘Talban Daura’, yayin da ake murnar babar sallah.

Sai dai kuma binciken da aka yi, ya nuna cewa Sarkin ya taba ba Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde wannan sarauta a lokacin da ya zo Najeriya a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel