Aljannar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan Ibrahim Babangida, kujerun ciki kamar zinare

Aljannar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan Ibrahim Babangida, kujerun ciki kamar zinare

  • Hotunan katafaren gidan da ke kan tsauni mallakar Janar Ibrahim Babangida ya haddasa cece-kuce a Facebook
  • Yayin da mutane da yawa suka yaba da kyawun ginin, wasu sun so su san yadda ake kula da shi
  • Hotunan sun kuma bayyana kyawawan kayayyaki masu ban mamaki da aka sanya cikin ginin wanda ya sa ya banbanta da wasu da dama

Hotunan babban gidan Ibrahim Babangida da ke Hilltop a Minna sun bazu a yanar gizo inda mutane da dama suka yi martani.

Hotunan da Ovation Magazine ta ɗauka sun nuna duka ciki da wajen gidan wanda ya ba mutane da yawa mamaki a yanar gizo.

Hotunan cikin katafaren gidan Ibrahim Babangida, kujerun ciki kamar zinare
Da dama na son sanin yadda ake kula da gidan Hoto: Ayo Oyeniyi
Asali: Facebook

Komai ya kayatu matuka

Da yake wallafa hotuna daga Mujallar a Facebook, Ayo Oyeniyi ya yi ikirarin cewa wani kamfanin gine-gine mai suna Julius Berger ne ya ba tsohon shugaban kasar gidan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Ya yi mamakin ko Babangida zai shiga cikin gidan kowane lokaci nan gaba. Hakanan hotunan sun nuna shuke-shuke masu kyau.

A gaban babban ginin akwai babban maadanar ruwa tare da tsiro da yawa suna ba da ruwa. Sai kasaitattun kujeru launin zinare suna ƙawata falon.

Kalli wallafar Facebook din a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Patrick A. Okohue ya ce:

"Domin wannan gidan ya tsira, tilas a mayar da shi zuwa otal a nan gaba, idan ba haka ba zai zama gidan beraye, kadangaru da sauran su a nan gaba."

Adekunle Idris Abdulraheem ya ce:

"Wani kudi suke amfani da shi wajen kula da wannan gida."

Gabriel Adewumi Adegoke ya ce:

"Aljanna Duniya, lokaci zai yi bayani."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock

A wani labarin, kasurgumin ‘dan kasuwan nan, Femi Otedola, yace Ibrahim Badamasi Babangida ya sa Dr. Goodluck Jonathan ya hau kujerar shugaban Najeriya.

Premium Times ta rahoto Femi Otedola yana cewa tsohon shugaban kasar ne ya ba Goodluck Jonathan shawarar ya zauna a kujerar Ummaru ‘Yar’adua.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng