Yadda Janar Babangida ya taimakawa Goodluck Jonathan ya dare kan kujerar Shugaban kasa

Yadda Janar Babangida ya taimakawa Goodluck Jonathan ya dare kan kujerar Shugaban kasa

  • Femi Otedola ya bada labarin yadda ya yi da Ibrahim Badamasi Babangida a 2010
  • Attajirin yace IBB ne ya sa Goodluck Jonathan ya dare kan kujerar shugaban kasa
  • Hakan ya faru ne lokacin da Ummaru ‘Yar’adu ya bar Najeriya babu wani shugaba

Abuja - Kasurgumin ‘dan kasuwan nan, Femi Otedola, yace Ibrahim Badamasi Babangida ya sa Dr. Goodluck Jonathan ya hau kujerar shugaban Najeriya.

Premium Times ta rahoto Femi Otedola yana cewa tsohon shugaban kasar ne ya ba Goodluck Jonathan shawarar ya zauna a kujerar Ummaru ‘Yar’adua.

Ummaru ‘Yar’adua ya bar Najeriya babu shugaban rikon kwarya

Otedola ya yabi yadda tsohon shugaban kasan na soja ya bi, ya shawo kan matsalar da Najeriya ta shiga a lokacin da Marigayi ‘Yar’adua yake jinya a ketare.

A littafinsa mai suna “business lessons” (darusan kasuwanci), da zai fito a watan Nuwamban bana, Otedola ya ce shi ne ya zama ‘dan-aiken Babangida.

Kara karanta wannan

Ni ne wanda IBB yake burin ya zama Shugaban kasa - Tsohon Hadimin Jonathan, Obasanjo

“A lokacin da Yar’Adua bai mika mulki ga mataimakinsa ba, ya tafi kasar waje neman magani, an shiga wani hali saboda an bar kasa babu shugaba.”

Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoton dazu, Femi Otedola ya ce wannan matakin da shugaban Najeriya na lokacin ya jawo zanga-zanga a fadin kasar nan.

Jonathan da Janar Babangida
Ibrahim Badamasi Babangida da Goodluck Jonathan Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Otedola ya zauna da IBB a Minna

“Ganin halin da ake ciki na dar-dar, sai na ce bari in yi wani abu da kai na. A farkon Fubrairun 2010, na ziyarci Minna, tare da Bola Shagaya domin yi wa IBB ta’aziyyar mutuwar mai dakinsa, Maryam.”
“Mun tattauna a kan abubuwa da-dama a gidansa, amma na fada masa akwai bukatar mu tattauna wani abu mai matukar muhimmanci da amfani.”

Kara karanta wannan

Sanatan Borno ya ja-kunnen Sojoji a kan maida tsofaffin ‘Yan ta’addan Boko Haram ‘yan lele

“Ya dauke ni zuwa dakin karatunsa, inda daga shi sai ni kawai. Sai na fada masa sha’anin kasar nan yana damu na, ya za a fita daga halin da ake ciki.”
“Femi, ku ba abokinku shawara cewa idan aka je taron majalisar zartar wa, FEC a fadar shugaban kasa a makon gobe, ya zauna a kujerar shugaban kasa.”

Shi kuwa Otedola ya na dawo wa Abuja, sai ya zauna da Jonathan, ya fada masa abin da IBB ya fada mani, sai ya ce mani zai yi tunani a kan wannan maganar.

Ibrahim Badamasi Babangida ya cika 80

Da ake magana wajen bikin taya Janar Ibrahim Badamasi Babangida murnar cika shekara 80 a Duniya ne sai Otedola ya dauko labarin abin da ya faru a 2010.

A lokacin da aka yi hira da shi kwanaki, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata mutane su zabi tsofaffin 'yan siyasa a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Idan zaben 2023 ya zo, Bola Tinubu bai da satifiket da zai nuna ya yi karatu inji Bode George

Asali: Legit.ng

Online view pixel