Zargin karkatar da dukiyar kasa: Gwamnonin jihohi 36 sun maka Buhari a kotu

Zargin karkatar da dukiyar kasa: Gwamnonin jihohi 36 sun maka Buhari a kotu

  • Gwamnonin Najeriya 36 sun kai karar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari gaban alkali
  • An tattaro cewa suna zargin Buhari da karkatar da kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati
  • Gwamnonin sun yi kira ga kotun koli da ta ayyana hakan a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya

Wani rahoto daga jaridar Punch ya nuna cewa Manyan Atoni Janar na jihohi 36 na kasar sun dauki wani mataki kan Ofishin Babban Atoni Janar Tarayya kan gazawar gwamnati wajen saka kudaden da ta kwato daga hannun barayin gwamnati a asusun tarayya.

An tattaro cewa gwamnonin jihohin na zargin gwamnatin Muhammadu Buhari da karkatar da kudaden da yawansu ya kai kimanin naira triliyan daya da biliyan dubu 800.

Zargin karkatar da dukiyar kasa: Gwamnonin jihohi 36 sun maka Buhari a kotu
Gwamnonin jihohi 36 na zargin gwamnatin tarayya da karkatar da dukiyar kasa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Har ila yau gwamnonin na zargin gwamnatin Buhari da kin saka kudaden a asusun tarayya tare da karkata akalar su zuwa wasu asusun ajiya na daban.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Sake Kashe Mutum 7 a Jos Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai

Kundin tsarin mulki ya ba da damar hade duk wasu kudaden shiga ta kasar a asusun bai daya ta yadda za a rika raba su kamar yadda doka ta tanada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin karar da ke gaban Kotun Koli mai lamba SC / CV / 395/2021, gwamnonin sun nemi kotun koli da ta bayyana cewa:

"Ya sabawa kundin tsarin mulki ga Shugaban kasa, ta hannun Ministan Kudi na Tarayya, AGF, ko wata hukuma tayi amfani ko ta raba ko ta kashe kudaden ba tare da an turata asusun tarayya ba."

Hakazalika sun nemi kotun da ta sanya gwamnatin ta dawo da kudaden asusun tarayya domin raba su kamar yadda doka ta tanada.

Sun kuma nemi a yi bincike saboda a gano adadin kudaden da aka samu daga cikin wadanda ake kwatowa daga barayin gwamnati tun daga 2015 lokacin Buhari ya karbi mulkin kasar, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Kungiyar gwamnonin kasar wanda Gwamna Kayode Fayemi ke jagoranta, sun tanadi tawagar kwararrun lauyoyi karkashin jagorancin Femi Falana domin wakiltar su a karar da suka shigar ranar Litinin.

Masu shigar da karar sun bayyana cewa:

"Tsakanin shekarar 2015 zuwa yau, FRN ta samu nasarar kwace kayayyakin kasa da kasa da na birni, tare da dawo da "kadarorin da aka sace" wanda jimlarsu ya ka NI,836,906,543,658.73, kimanin kadarori 167, Motoci 450, manyan motoci da kago 300, da gangunan danyen mai 20,000,000 wanda darajarsu ta kai sama da miliyan N450m."

RFI Hausa ta kuma ruwaito cewa suna zargin Buhari da take hakkokin jihohin kasar a yayin da yace yana yaki da cin hanci da rashawa.

Dokar kasa ta baiwa kotun koli damar sauraron shari'a tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya akan lamuran da suka shafi kundin tsarin mulki.

A wani labari na daban, babban kamfanin man Najeriya watau NNPC, zai zama kamfanin ‘yan kasuwa nan da watanni shida, gwamnatin tarayya ta bayyana haka.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: PDP ta bukaci a gaggauta tsige Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe

Channels TV ta rahoto cewa mai girma karamin Ministan harkokin man fetur na kasa, Timipre Sylva, ya yi magana da manema labarai a garin Abuja.

Da yake bayani a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, Timipre Sylva yace gwamnati ta kafa kwamitin da zai yi aikin damka wa ‘yan kasuwa NNPC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel