Da Duminsa: PDP ta bukaci a gaggauta tsige Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe

Da Duminsa: PDP ta bukaci a gaggauta tsige Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe

  • Jam'iyyar PDP ta maka gwamna Buni a kotu bisa zarginsa da saba ka'idar tsarin mulkin Najeriya
  • PDP ta bukaci kotu da ta tsige gwamnan, kuma ta gaggauta maye gurbinsa da 'yan takarar PDP da suka fadi a zaben 2019
  • PDP ta ce bai kamata gwamnan ya rike matsayin shugaban jam'iyya na riko da kuma kasancewarsa gwamna

Jam'iyyar PDP ta fara daukar matakin doka na tsige gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni daga mukaminsa bisa zargin sabawa kundin tsarin mulki da ya hana shugaba gudanar da ofisoshi biyu a lokaci daya, THISDAY ta ruwaito.

PDP a cikin karar da aka shigar ranar 12 ga watan Agusta, tana zargin Buni ya sabawa sashi na 183 na kundin tsarin mulki saboda a matsayin gwamna ya yarda ya zama Shugaban Kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC.

Da Duminsa: PDP ta bukaci a gaggauta sauki Buni a matsayin gwanan Yobe
Mambobin PDP | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Getty Images

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Umar Damagum da Baba Aji a ta hanyar Emeka Etiaba (SAN), sun dage cewa Buni ya zama ba gwamna ba daga lokacin da ya yarda ya karbi matsayin Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC.

Don haka masu shigar da karar sun nemi kotun da ta umarci babban alkalin jihar Yobe ko wani babban mutum da ke kusa da babban alkalin da ya gaggauta rantsar da Damagum da Aji a matsayin Gwamna da Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe.

PDP ta bayyana haka ne saboda Damagum da Aji su ne ‘yan takarar jam’iyyar PDP suka zo na biyu a zaben gwamna na 2019.

Ta ina maganar ta samo asali?

Wannan batu ya zo ne a cikin damuwar da ta taso bayan hukuncin babbar kotun, wacce ta tabbatar da nasarar Rotimi Akeredolu a matsayin gwamnan jihar Ondo, in ji The Cable.

A cikin hukuncin 4:3 wanda ya tabbatar da Akeredolu a matsayin gwamnan Ondo, kotun koli ta tado da magana kan cancantar Buni na gudanar da babban taron APC da tsayar da 'yan takara.

Da yake tsokaci game da batun, Festus Keyamo, karamin ministan kwadago, ya ce domin jam'iyyar ta guji rikicin kotu, ya kamata APC ta dakatar da babban taron ta kuma maye gurbin Buni.

Amma jam'iyyar ta yi watsi da maganarsa.

Magnus Abe, tsohon sanata kuma mamba a hukumar kamfanin mai na kasa (NNPC), da Ovie Omo-Agege, mataimakin shugaban majalisar dattijai, suma ba su yarda da matsayar Keyamo ba.

Yahaya Bello ne matashin dan takarar da zai iya gyara Najeriya, in ji wani sanatan Kogi

A wani labarin, Sanata Smart Adeyemi (APC – Kogi ta yamma) ya bayyana Yahaya Bello a matsayin dan takarar shugaban kasar Najeriya da ya fi cancanta da gadon shugaba Buhari a zaben 2023, kuma ya daga Najeriya ta fuskar karfin tattalin arzikin duniya.

Sanatan na Kogi ya bayyana gwamnan na Kogi a matsayin gwamna matashi mai dimbin kuzari, da basirar ilimi da sanin makamar aiki tare da tarihi mai kima, ya kara da cewa yana da abin da zai kai kasar nan zuwa tudun na tsira, Daily Sun ta ruwaito.

Da yake rokon ‘yan Najeriya da su yi la’akari da burin zama shugaban kasa na Gwamna Bello, Sanata Adeyemi ya ce idan aka ba shi dama gwamnan zai hada da nasarorin gwamnatin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel