NNPC zai tashi aiki a Najeriya nan da watanni 6 inji Shugaban NNPC, Mele Kyari

NNPC zai tashi aiki a Najeriya nan da watanni 6 inji Shugaban NNPC, Mele Kyari

  • Hukumar man Najeriya na NNPC zai zama kamfanin NNPC Limited
  • Hakan na zuwa ne bayan Muhammadu Buhari ya shigo da dokar PIB
  • NNPC za ta koma karkashin kulawar ‘yan kasuwa nan da wata shida

Abuja - Babban kamfanin man Najeriya watau NNPC, zai zama kamfanin ‘yan kasuwa nan da watanni shida, gwamnatin tarayya ta bayyana haka.

Channels TV ta rahoto cewa mai girma karamin Ministan harkokin man fetur na kasa, Timipre Sylva, ya yi magana da manema labarai a garin Abuja.

Da yake bayani a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, Timipre Sylva yace gwamnati ta kafa kwamitin da zai yi aikin damka wa ‘yan kasuwa NNPC.

Sylva yace Gwamnatin tarayya za ta rike duk wasu hannun jari a kamfanin NNPC Limited. Ma’aikatar kudi za ta lura da hannun jarin gwamnatin.

Kara karanta wannan

Farashin litar man fetur zai iya kai N300 bayan Shugaba Buhari ya sa hannu a dokar PIB

Ministan yake cewa duk da dokar PIB da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kai ta fara aiki, za a cigaba da biyan tallafin man fetur.

Da yake bayani a wajen zanta wa da manema labarai, shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, yace kadarorin NNPC za su koma hannun sabon kamfanin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari, Shugaban NNPC, da wasu
Mele Kolo Kyari; Ben van Beurden; Mohammadu Buhari; da Timipreye Silva a Abuja Hoto: thecitizenng.com
Asali: UGC

Abin da hakan ya ke nufi

Jaridar The Cable ta ke cewa Malam Mele Kolo Kyari ya nuna NNPC za ta rabu da kadarorin da suka zama wa gwamnati alakakai a sabon tsarin.

“Idan muka koma kan NNPC, doka ta ce hukumar za ta koma karkashin kamfanin ‘yan kasuwa, hakan na nufin zai zama karkashin ‘yan kasuwa."
“Wannan kamfani zai rika biyan gwamnatin Najeriya haraji, riba, ya ba masu hannun jari ribar da aka samu daga kasuwanci. Ba haka abin yake a yau ba.”

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta ce a karbe N241m da aka karkakatar daga ofishin Hadimin Shugaba Buhari

Kamar yadda Mele Kyari ya fada, NNPC zai zama karkashin kulawar ‘yan waje, kuma za a rage girman kamfanin, sannan ana sa ran a fi cin moriyarsa.

A makon nan, kun samu rahoto gwamnatin tarayya za ta mallakawa ‘Yan kasuwa wasu daga cikin manya-manyan filayen tashi da saukar jirgin saman Najeriya.

Gwamnati ta na sa rai hakan ya sa a gyara filayen jiragen kasar, sannan mutane su samu abin yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel