Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

  • Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, yace an samu raguwar ayyukan yan bindiga sosai a jihar
  • Masari ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyin wakilan hukumar dillancin labarai ta Najeriya ranar Lahadi
  • Gwamnan ya sake jaddada cewa aikin samar da tsaro a jihar Katsina ya rataya a wuyan kowa

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari, yace sam babu wani siddabaru da gwamnatinsa ta yi wajen rage ayyukan yan bindiga a Katsina, kamar yadda aminiya ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga wakilan hukumar dillancin labarai ta Najeriya (NAN) a Katsina ranar Lahadi, kamar yadda premium times ta ruwaito

Masari ya bayyana cewa gudummuwa da kowa ke bayarwa a jihar kama daga sarakunan gargajiya, jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki wajen nemo hanyar warware matsalar shine yake haifar da ɗa mai ido.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka Sun Kashe Mutane da Dama Tare da Sace Wasu a Sokoto

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari
Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Gwamna Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wane matakai gwamnatin Katsina ta ɗauka?

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Masari ya kara da cewa tun da fari ya bada umarnin duk mutanen dake cikin daji waɗanda ba ruwansu da aikata laifuka su dawo cikin gari.

Masari yace:

"Na ba da umarnin cewar dukkan mutanen kirki da ke zaune a dazuka su fito su shiga cikin sauran al’umma a kauyuka da manyan garuruwa da birane don gudun yi musu kudin goro."
"Saboda haka, yanzu ba mu da sauran mutanen da ke zaune a daji. Duk wanda ka gani a daji yanzu to ko dai dan bindiga ne ko kuma bata gari."
“Hatta tsofaffin da har yanzu suke cikin daji su ma ’yan bindiga ne wadanda ke fitowa su aikata ta’asa sannan su koma, mun cimma nasara sosai wajen magance matsalar tsaro a Jiharmu"

Gwamnati zata ginawa yan gudun hijira gidaje

Kara karanta wannan

Gwamna Masari ya yi barazanar maaka hukumar Kwastam a kotu kan kashe-kashe a Katsina

Gwamna Masari ya kara da cewa gwamnatinsa zata gina gidaje domin samar da muhalli ga waɗanda lamarin rashin tsaro ya raba da gidajensu.

Ya kuma kara jan hankali cewa tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar Katsina alhaki ne da yake kan kowa.

A wani labarin kuma Khalifan Tijjaniyya Ya Magantu Kan Kisan da Aka Yiwa Zakirai Fiye da 20 a Jos

Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga gwamnatin tarayya, gwamnatin Filato da jami'an tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka kashe matafiya fiye da 20 a Jos.

Tsohon sarkin Kano yace ya zama wajibi gwamnati ta sauke amanar da Allah ya bata na kare rayukan al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262