Babu Wasu Yan Bindiga da Ba'a San Su Ba, Gwamna Ya Zargi Wasu Mutane a Jiharsa
- Gwamnan Ebonyi, David Umahi, ya zargi wasu mazauna jihar da kuma sauran jihohin yankin kudu-gabas da rura wutar rikici
- Gwamnan yace da waɗanda ake kashewa da kuma masu aikata kisan duk mutanen yankin ne
- Ya kara da cewa jami'an tsaro dake bada rayuwarsu domin kare al'umma ba su dace ana kashe su ba
Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya zargi wasu mutane a yankin kudu maso gabas da rura wutar rikici a yankin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Gwamnan ya yi wannan zargi ne yayin da yake martani kan dokar zaman gida da yan awaren IPOB suka saka a yankin.
Haramtacciyar kungiyar ta bayyana kulle yankin a kowane mako domin nuna fushinta da kame shugabansu, Nnamdi Kanu.
Gwamnan zai kori ma'aikata da kwace shaguna
Umahi ya gargaɗi mutanen jiharsa kan yin ɗa'a ga dokar, inda ya yi barazanar zai kori duk wani ma'aikaci da ya bi umarnin ƙungiyar IPOB.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakazalika gwamnan yace duk wani shago da aka rufe saboda bin dokar ta ranar Litinin zai rasa damar mallakar wurin.
Gwamna Umahi yace:
"Na bada umarnin a sallami duk wani ma'aikaci da ya ƙi zuwa aiki da kuma ma'aikatan wuraren da muke aikin ginawa suma a kore su nan take idan basu fito aiki ba."
"Kowane shago ko wurin kasuwanci da masu shi suka ki buɗewa don yin kasuwancin su, zasu rasa damar mallakar wurin, kuma inason kowa yasan wannan umarnin."
Babu wasu yan bindiga da ba'a san su ba
Gwamnan ya kuma yi kira ga mutanen jihar Ebonyi da su fito su bayyana yadda lamarin rikicin yake kara muni domin a ɗauki mataki.
Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamnan Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jiharsa
The cable ta ruwaito Umahi yace:
"Ba wanda zaiso a cigaba da yaki a kudu maso gabas kuma ya kamata mutanen mu musamman matasa su tashi tsaye su ɗauki mataki kan haka."
"Babu wasu yan bindiga da ba'a san su ba domin waɗanda ake kashewa da waɗanda suke kisan duk mazauna yankin ne."
Gwamna Umahi ya ƙara da cewa jami'an tsaro waɗanda suke bada rayuwarsu domin kare mutane basu cancanci ana kashe su ba.
A wani labarin kuma Zamu Ceto Malamai da Daliban Kwalejin Bakura da Aka Sace, Matawalle Ya Yi Alkawari
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya nuna rashin jin dadinsa bisa sace ɗalibai 15 tare da wasu malamai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura.
Matawalle, a wata sanarwa da kakakinsa, Yusuf Idris, ya fitar ranar Litinin, yace alhakin gwamnatin jihar ne ta kubutar da su cikin koshin lafiya.
Asali: Legit.ng