Shugabancin 2023: Buni, Bagudu, Abubakar sun hadu da Bankole a Abeokuta

Shugabancin 2023: Buni, Bagudu, Abubakar sun hadu da Bankole a Abeokuta

  • Gwamna Mai Mala Buni da sauran jiga-jigan APC sun gana da Cif Alani Bankole, a Abeokuta a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta
  • Ana ganin wannan ganawar da shugaban na kudu maso yamma na da alaka da babban zaben 2023 a kasar
  • Ku tuna cewa tawagar ta kai irin wannan ziyarar ga tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Rashidi Ladoja, a gidansa na Ibadan

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya ninka a matsayin shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC ya yi wata ganawar sirri da mahaifin tsohon kakakin majalisar wakilai, Cif Alani Bankole, a Abeokuta, a ranar Litinin.

Tawagar, wacce ta ziyarci gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun a gidansa na Iperu-Remo kan rasuwar mahaifinsa, sun zarce Abeokuta inda aka gudanar da taron na sirri.

Kara karanta wannan

Bikin Sauya Sheka: Gwamnonin Jam'iyyar APC Uku Sun Gana da Wani Tsohon Gwamna

Shugabancin 2023: Buni, Bagudu, Abubakar sun hadu da Bankole a Abeokuta
Shugabannin APC, Buni, Bagudu da Abubakar sun hadu da Bankole a Abeokuta Hoto: APC
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta cewa tawagar da Buni ya jagoranta sun ziyarci likitan ilimin a matsayin wani bangare na tuntuba da shugabannin siyasa na Kudu maso Yamma gabanin babban zaben 2023.

Tawagar ta kai irin wannan ga ziyarar tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Rashidi Ladoja, a gidansa na Ibadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauya sheka na zuwa yayin da Buni da shugabannin APC ke ganawa da Ladoja gabanin shekarar 2023

Ku tuna cewa Legit.ng ta ruwaito Buni tare da wasu gwamnoni biyu sun gana da tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja a gidan sa dake Ibadan, jihar Oyo.

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, takwaransa na jihar Jigawa, Abubakar Badaru da Sanata Fatai Buhari mai wakiltar mazabar Oyo ta arewa, sun halarci taron. Taron wanda aka yi cikin sirri rahoton ya dauki kimanin awa daya.

Kara karanta wannan

Tana shirin kwabewa yayin da PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe

Legit.ng ta tattaro cewa mai magana da yawun tsohon gwamnan, Alhaji Lanre Latinwo, ya ce 'yan siyasar ba su yi karin haske kan abin da aka tattauna ba

2023: Fitaccen jigon APC ya bayyana yankin da zai samar da wanda zai gaji Buhari

A wani labarin, Kashim Ibrahim-Imam, jigo a jam'iyyar ya rufe hasashen fitowar dan takarar shugaban kasa na APC daga shiyyar kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa dan takarar gwamnan na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sau biyu, wanda a yanzu jigo ne na APC, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, a wani shiri na Arise TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel