Bikin Sauya Sheka: Gwamnonin Jam'iyyar APC Sun Shiga Ganawar Sirri da Wani Tsohon Gwamna
- Gwamnonin APC uku dake kan Mulki sun dira gidan tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja, ranar Lahadi
- Rahotanni sun bayyana cewa ana tsammanin gwamnonin sun gana da shi ne domin jawo hankalinsa ya koma APC
- Gwamna Mai Mala Buni na Yobe shi ya jagoranci sauran takwarorinsa biyu zuwa gidan Ladoja a Ibadan
Oyo - Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC uku a Ibadan, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Taron wanda aka shafe sama da awanni uku ana yinsa ya gudana ne a gidan Ladoja dake Ibadan, babban Birnin Oyo.
Duk da cewa babu wani cikakken bayani game da abinda suka tattauna, amma ana tsammanin ganawar tana da alaƙa da sauya sheka zuwa APC.
Wane gwamnoni ne suka halarci taron?
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Premium times ta ruwaito gwamnonin APC da suka halarci taron sun haɗa da, Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na APC.
Sauran sun haɗa da gwamnan jigawa, Abubakar Badaru, da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu.
Me aka tattauna a ganawar?
Wata majiya ta shaidawa hukumar dillancin Najeriya (NAN) cewa gwamnonin sun je gidan Ladoja ne domin tattauna matsalar tsaro da kuma jawo hankalinsa zuwa APC.
"Suna son ya sauya sheka zuwa jam'iyyarsu ta APC ne," inji wani makusancin ɗaya daga cikin jiga-jigan siyasa, wanda ya nemi ya ɓoye sunansa.
A halin yanzun duk wani kokari na jin ta bakin Mr. Ladoja ko kuma gwamnonin na APC ya ci tura.
Ganawar ta su ta kasance cikin sirri kuma bayan fitowa sun ki bayyana sakamakon taron nasu.
A wani labarin kuma Wata Sabuwa, Shugaba Buhari Ya Killace Kansa Bayan Dawowa Daga Landan
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , tare da jami'an gwamnati da suka raka shi sun killace kansu bayan shafe sama da makwanni biyu a Landan.
Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shine ya tabbatar da haka ga Channels tv ranar Lahadi.
Shehu ya bayyana cewa shugaban ya ɗauki wannan matakin ne domin biyayya ga dokokin hukumar dakile yaɗuwar cututtuka (NCDC).
Asali: Legit.ng