Muna tsakar tattaunawa da Gwamnonin PDP 2 da za mu shigo da su APC inji Jigon Jam’iyya

Muna tsakar tattaunawa da Gwamnonin PDP 2 da za mu shigo da su APC inji Jigon Jam’iyya

  • Kashim Ibrahim-Imam yace Rashidi Ladoja yana daf da shigo wa Jam’iyyar APC
  • ‘Dan siyasar na Borno ya bayyana cewa APC ta zauna da wasu Gwamnoni na PDP
  • Ibrahim Imam ya sa rai a samu karin gwamnonin adawa biyu da za su shigo APC

Daya daga cikin manyan jam’iyyar APC, Alhaji Kashim Ibrahim-Imam, ya bayyana cewa suna tattauna wa da wasu cikin gwamnonin jam’iyyar adawa.

Kashim Ibrahim-Imam: Za mu yi babban kamu

A ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, jaridar Daily Trust ta rahoto Kashim Ibrahim-Imam yana cewa suna neman jawo wasu gwamnoni biyu da ke PDP.

Kashim Ibrahim-Imam bai kama sunayen wadannan gwamnoni da jam’iyyar APC ta ke zawarci ba.

Haka zalika, Ibrahim-Imam ya tabbatar da haduwar manyan APC da tsohon gwamnan jihar Oyo, Alhaji Rashidi Ladoja, wanda yace kwanan nan zai bi tafiyarsu.

Kara karanta wannan

Bikin Sauya Sheka: Gwamnonin Jam'iyyar APC Uku Sun Gana da Wani Tsohon Gwamna

Jam’iyyar APC ta jawo Rashidi Ladoja ne bayan ta yi wani zama da shi a Ibadan. Ladoja wanda ya yi mulki daga 2003 zuwa 2007 yana da magoya-baya har gobe.

Da yake magana da gidan talabijin na Arise TV a ranar Litinin, Ibrahim-Imam ya tabbatar da cewa za a samu karin wasu gwamnonin da za su shigo jirgin APC.

Jam’iyyar APC
Jam’iyyar APC ta na kamfe a Borno Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Ibrahim-Imam shi ne ya yi wa jam’iyyar PDP takarar kujerar gwamna a jihar Borno a zabukan 2015 da 2019, kafin shi ma ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

‘Dan siyasar ya tabo batun mika mulki ga Ibo a 2023, yace hakan zai yi wahala domin jam’iyyarsu ta APC ba ta da karfi sosai a Kudu maso gabas da kudu maso kudu.

Kara karanta wannan

Neman a tsige Buni daga kujerar gwamna: APC ta yi wa PDP wankin babban bargo

PDP za ta sake rasa wani gwamna?

Wannan bayani da Imam ya yi, ya saba wa matsayar PDP kamar yadda sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan, ya shaida wa manema labarai a makon jiya.

Ologbondiyan yace a taron gwamnonin da PDP ta yi, kowa ya tabbatar da cewa ba zai sauya-sheka ba.

APC mai mulki ta na kokarin rage karfin APC ne bayan ta raba ta da gwamnoni uku; David Umahi a Ebonyi, Ben Ayade a Kuros Riba da Bello Mutawalle a Zamfara.

Da yake karin bayani, Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, yace ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki ne domin karfafa hadin kan 'yan siyasan jiharsa.

Gwamnan ya bayyana yadda ya mori abubuwan alheri daga shugaba Muhammadu Buhari duk da a da yana PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel