Wannan ba shine farko ba: Izala ta yi martani kan kashe Musulmai da aka yi a Jos

Wannan ba shine farko ba: Izala ta yi martani kan kashe Musulmai da aka yi a Jos

  • Sheikh Jingir ya magantu kan yadda aka kashe wasu matafiya musulmai a garin Jos jiya Asabar
  • Malamin ya bayyana kukansa, tare da kiran mutane a fadin Najeriya da su kwantar da hankulansu
  • Ya kuma bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar mataki kan wannan mummunan lamari da ya faru

Jihar Filato - Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Shiekh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga Musulmi a fadin kasar nan da su kwantar da hankalinsu bayan kisan matafiya musulmai da aka yi a Jos ranar Asabar.

Ya yi wannan kira ne a wata hira da manema labarai ranar Lahadi a Jos, Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito a baya cewa, wasu matafiya musulmai 25 aka kashe a Jos, Jihar Filato, har yanzu ba a ga wasu da dama ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Ya ce duk da kisan yana da zafi da bakin ciki, amma bai kamata mutane su dauki doka a hannun su ba.

Sai dai malamin ya bukaci a gaggauta kamawa tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Sheikh Jingir ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su tabbatar da adalci ga matafiyan da basu ji ba basu gani ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar Izala ta yi martani bisa kashe Musulmai da dama a Jos
Sheikh Sani Yahaya Jingir | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Ya ce:

“Wannan ba shi ne karon farko da aka kama matafiya Musulmi aka kashe su a kan manyan hanyoyi ba.

“Me ya sa mutane za su ci gaba da aikata irin wannan danyen aikin kuma su tafi salin-alin? ba daidai bane.

Sheikh Jingir, ya ce a duk lokacin da gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai binciki wata matsala, da kyar za a yi wani abu game da sakamakon kwamitin, tare da fatan wadanda suka aikata wannan aikin ba za su tsira ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

Babban malamin na addinin Musulunci ya yabawa dukkan hukumomin tsaro kan irin martanin da suka yi cikin gaggawa.

Ya ce:

"Na kuma yaba da kokarin Gwamna Simon Lalong, Gwamna [Rotimi] Akeredolu da Shugaba [Muhammadu] Buhari, don tabbatar da cewa lamarin bai yi nisa ba."

Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe

Kungiyar fafutukar kare hakkin musulmai (MURIC) ta yi kira da a gaggauta kame gaba ɗaya waɗanda suka aikata kisan musulmai matafiya a Jos, inda ta kira su da "Mayakan kiristoci a Jos."

Daily Nigerian ta ruwaito cewa matafiya musulmai 25 wasu sojojin ƙungiyar kiristanci suka kashe a Rukaba, jihar Filato ranar Asabar.

A wani jawabi da daraktan MURIC, Ishaq Akintola, ya fitar, ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa musulmai, tare da kira ga gwamnati ta kame waɗanda suka aikata kisan.

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

A wani labarin, Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.

Wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel