Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Ceto Karin Mutum 7 Daga Cikin Musulman da Aka Kaiwa Hari a Jos

Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Ceto Karin Mutum 7 Daga Cikin Musulman da Aka Kaiwa Hari a Jos

  • Rundunar sojojin Operation Safe Haven sun sake ceto karin mutum 7 daga cikin waɗanda harin Jos ya rutsa da su
  • Sojojin sun bayyana cewa sun kai mutanen wani wuri mai tsaro domin cigaba da duba lafiyar su
  • Wannan ya biyo bayan wani hari da aka kaiwa matafiya da suka dawo daga zikirin shekara-shekara a Bauchi

Plateau - Sojojin Najeriya a jihar Filato na Opertaion Safe Haven sun bayyana cewa sun ceto ƙarin mutum 7 daga cikin waɗanda harin Jos ya rutsa da su.

Hakanan kuma hukumar yan sanda ta sanar da cewa ta samu nasarar kara kubutar da wasu mutum 33 daga cikin musulmai da lamarin ya rutsa da su, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Sufeto janar na yan sandan ƙasar nan, Usman Alkali Baba, ranar Lahadi, ya bada umarnin tura jami'an yan sanda wurin lamarin ya faru domin bincike.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka Sun Kashe Mutane da Dama Tare da Sace Wasu a Sokoto

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da aka kaiwa matafiya a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta arewa, jihar Filato.

Punch ta ruwaito cewa da farko sojojin sun kubutar da mutum 12 yayin harin, wanda yayi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 25, wasu da dama suka jikkata.

Sojoji Sun ceto karin mutum 7
Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Ceto Karin Mutum 7 Daga Cikin Musulman da Aka Kaiwa Hari a Jos Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutanen sun dawo daga zikiri a Bauchi

Rahotanni sun nuna cewa matafiyan sun dawo ne daga zikirin shekara-shekara a jihar Bauchi kuma suna kan hanyar zuwa Ikare jihar Ondo.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Operation Safe Haven, Manjo Ishaku Takwa, ya fitar yau Lahadi, yace waɗanda aka ceto ɗin an kai su wani wuri mai tsaro domin kulawa da lafiyarsu.

Sanarwar tace:

"A yau Lahadi sojojin Operation Safe Haven sun sake ceto karin mutum 7 daga cikin matafiyan da aka kaiwa hari a Rukuba jiya Asabar."

Kara karanta wannan

Wannan Shiryayyen Kisa Ne, Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai da Kisan Musulmai a Jos

"A halin yanzun sojojin sun kai waɗanda suka ceto ɗin wani wuri mai tsaro domin cigaba da kula da lafiyarsu."
"Hakanan kuma sojojin na cigaba da binciken gano tare da ceto sauran waɗanda suka bata yayin harin.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan mulumai a Jos yace harin shiryayye ne ga abinda aka hara.

Shugaban ya kuma umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kamo duk wani.mai hannu a kisan matafiyan, ya kuma kara da cewa baya son kurkure kan lamarin.

Buhari yace sanannen abu ne jihar Filato na ɗaya daga cikin jihohin da rikitin addini da na makiyaya da manoma ya saba faruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel