A karon farko, gwamnatin Buhari ta ware wa 'yan sanda kudin sayen man fetur
- Gwamnatin Buhari ta samar da makudan kudade ga rundunar 'yan sanda domin sayen man fetur
- Wannan ne karo na farko da aka ware makudan kudade da suka kai biliyoyi domin sayen man fetur
- Hakazalika, ministan harkokin 'yan sanda ya magantu kan sabon tsarin albashin 'yan sanda
Gwamnatin Najeriya ta amince da ware naira biliyan hudu na man motocin aiki na 'yan sanda a fadin jihohi 36 na kasar hadi da Abuja, BBC Hausa ta ruwaito.
An ruwaito cewa, ministan ma’aikatar harkokin 'yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ne ya tabbatar da haka a Abuja a ranar Talata.
Ministan ya ce kudin wanda aka ware a kasafin 2021 shi ne karon farko da aka ware wa 'yan sanda kudin fetur kaso mai tsoka a kasar.
An kara samar da sabbin ci gaba a hukumar 'yan sanda
Ya kara da cewa Majalisar zartarwa ta tarayya a kwanakin baya ta amince da Ayyukan Musamman na 'yan sanda don inganta gaskiya da rikon amana tare da zama karin hanyar samar da kudade don inganta ayyukan 'yan sanda, in ji Daily Trust.
Da aka tambaye shi lokacin da sabon tsarin albashin jami’an ‘yan sanda wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawari zai fito, sai ya ce umurnin Shugaban kasa ga Hukumar Biyada Albashi ta Kasa don samar da sabon tsarin albashi mai inganci zai fito nan ba da jimawa ba.
An samar wa sojojin da ke yakar 'yan Boko Haram jirgin yawo lokacin hutu
A wani labarin daban, rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa za a samar da jirgin saman zirga-zirga ga sojoji da manyan jami'ai a fagen daga wadanda aka ba izinin ficewa na wucin gadi da nufin zuwa ganin danginsu yayin da suke kan aiki.
Jaridar TheCable ta ba da rahoton cewa izinin ficewar, a yaren sojoji, izini ne na barin sashin aiki na dan wani lokaci.
Legit.ng ta tattaro cewa mafi yawan sojoji da jami'ai da aka tura daga sassa daban-daban na kasar zuwa rundunar Operation Hadin Kai a arewa maso gabas suna tafiya daruruwan kilomita lokacin da suke kan izinin ficewa na wucin gadi domin ganin danginsu.
Asali: Legit.ng