IPOB: An kashe jami'ai 4 a yayin da 'yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda

IPOB: An kashe jami'ai 4 a yayin da 'yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda

  • Rahotanni sun ce an kashe jami’an ‘yan sanda hudu a wani artabu tsakanin ‘yan sanda da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba
  • Wasu da ake zargin yan asalin yankin Biafra (IPOB) ne suka aiwatar da harin wanda ya faru a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, a ofishin 'yan sanda da ke Nnewi, jihar Anambra
  • Daraktan yada labarai na IPOB, Emma Powerful ya ce za a takaita zirga -zirgar mutane da ababen hawa a duk fadin kasar Biyafara duk ranar Litinin, har sai an sallami jagoran nasu ba tare da wani sharadi ba

Anambra- Harin da ake zargin wasu 'yan asalin Biafra (IPOB) ne suka kai ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an' yan sanda hudu.

Harin wanda ya faru a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, ya kasance ne sakamakon artabun da ya barke tsakanin ‘yan sanda da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a ofishin ‘yan sanda da ke Nnewi, jihar Anambra.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga makare cikin motoci 7 sun kai hari wani sabon ofishin 'yan sanda

IPOB: An kashe jami'ai 4 a yayin da 'yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda
Lamarin ya haifar da damuwa a zukatan shugabannin yankin Hoto: @Chief Willie Obiano
Asali: Facebook

A wata hira da gidan talabijin na Channels TV, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce har yanzu ofishinsa bai samu cikakken rahoto kan lamarin ba.

Ya kara da cewa 'yan sanda sun yi fafatawa da maharan.

Majiyoyi sun sanar da cewa, 'yan bindigar sun kai farmaki kan rundunar 'yan sanda a ranar Litinin da rana kuma suka yi artabu da jami'an tsaron.

An shafe sama da sa’a guda ana arangama da maharan wadanda suka zo kai farmaki ofishin 'yan sanda a cikin motoci bakwai, Channels TV ta nuna.

Wannan harin ya kara haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin yayin da suka tsere don samun mafaka duk da cewa sojojin sun bi bayan maharan ba tare da samun nasara ba.

Kungiyar ta bakin Daraktan yada labaranta, Emma Powerful ta ce za a takaita zirga -zirgar mutane da ababen hawa a duk fadin kasar Biyafara duk ranar Litinin, daga jiya, 9 ga watan Agusta, har sai an sako Nnamdi Kanu ba tare da wani sharadi ba, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: APC ta aike da sako ga 'yan Najeriya yayin da ‘yan sanda suka karbe hedikwatarta a Abuja

Hakazalika,ana zaton cewa harin ramuwar gayya ce daga kungiyar da aka haramta bayan kashe wasu membobin su biyu a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta.

'Yan ta'addan IPOB sun kone fasinja kan karya dokar zaman gida a Imo

A gefe guda, mambobin IPOB sun kone wani fasinja mai suna Nkwogu a karamar hukumar Ahiazu Mbaise dake jihar Imo sakamakon karya dokar zaman gida na dole da suka saka a ranar Litinin.

Tuni dai dukkannin harkokin kasuwanci suka tsaya a yawancin sassan jihohin kudu yayin da mazauna yankin suke bin dokar da aka saka, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel