Sojoji sun hallaka yan ta'addan IPOB 6, an damke 13, an kwace AK47 guda 19
- Jami'an tsaron Najeriya na cigaba da samun nasarori kan yan bindiga da yan ta'adda
- Da alamun matsalar tsaro zai zo karshe idan aka cigaba da samun irin wadannan nasarori
- An samu nasarar damke babban kwamanda a kungiyar IPOB/ESN
Rundunar Sojojin Najeriya tare da hadin kan sauran jami'an tsaro a kudu maso gabas inda suka hallaka kwamandan IPOB da yaransa biyar bayan artabu da sukayi a Nkanu, jihar Enugu.
Hakazalika jami'an sun damke mutum 13 cikin yan kungiyar rajin ballewa daga Najeriya.
Mukaddashin diraktan yada labarai na hedkwatar tsaro, Birgediya Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai kan nasarorin da suka samu ranar Alhamis, rahoton Vanguard.
Yace a hare-haren da suka kai kudu maso gabas:
"An hallaka wani kwamandan ESN kuma an damke daya. Gaba daya, an hallaka yan IPOB/ESN shida yayinda aka damke mutum 13."
Wannan nasara ya biyo bayan harin kwantan bauna da jami'an tsaro suka kaiwa yan ta'addan da suka kashe DPO na yan sanda a garin Omuma dake karamar hukumar Orlu East, a jihar Imo.
Bayan haka, jami'an tsaro sun damke wani kasurgumin dan IPOB/ESN mai suna Obumneka a garin Umeli Amaraku a karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar Imo. An kamashi da makamai da harsasai.
Yace:
"Sojoji sun kai hari mabuyar IPOB/ESN dake garin Amaechi Idod a karamar hukumar Nkanu na Enugu da Nguzu Edda a karamar hukumar Afikpo a Ebonyi."
"Sojojin sun kwace bindigar AK-47 guda 19, bindigogin gargajiya 2, bindigar G3, dss."
Asali: Legit.ng