Shugaba Buhari ya kai wa jagoran APC, Bola Tinubu ziyara har gidansa a Landan

Shugaba Buhari ya kai wa jagoran APC, Bola Tinubu ziyara har gidansa a Landan

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Bola Tinubu sun hadu a kasar Ingila
  • Muhammadu Buhari ne ya taka da kansa, ya kai wa Bola Tinubu ziyara har gida
  • Buhari ne na biyu da aka gani tare da Tinubu yayin da ake rade-radi bai da lafiya

London - Mai girma shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara dakansa zuwa gidan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Landan, kasar Ingila.

Buhari ya taka, ya je gidan Tinubu

Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad ya fitar da hotunan wannan gana wa da aka yi tsakanin manyan kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari, Muhammadu Buhari ya ziyarci tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Bashir Ahmaad da ya fitar da hotunan a Facebook, bai yi karin bayani a game da abin da ya kai Mai girma shugaban kasar zuwa inda jagoran na APC yake ba.

Daily Trust ta lura Bola Tinubu ya na rike ne da sandar da yake dogara wa. Za kuma a ga cewa ya rufe fuskarsa da takunkumi domin guje wa cutar COVID-19.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi ma Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya shafe kwanaki 18 a Landan ya na sanye da tsummar rufe fuska yayin da aka dauke su hoto a ranar Alhamis.

Shugaba Buhari ya kai wa jagoran APC, Bola Tinubu ziyara har gidansa Landan
Shugaba Buhari da Bola Tinubu Hoto: @Bashamad
Asali: Facebook

Kamar yadda Femi Adesina ya sanar a baya, Buhari ya zo Ingila ne domin ya halarci taron GPE 2021-2025, sannan kuma ya samu damar hadu wa da likitocinsa.

Bola Tinubu bai da lafiya?

Legit.ng ta fahimci cewa wannan ziyara da shugaban Najeriya ya kai wa Bola Tinubu ta biyo bayan haduwarsa da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kai wa mai gidansa ziyara a makon jiya, a lokacin da ake ta rade-radin bai da lafiya, ya na jinya a wani asibiti da ke kasar Ingila.

Hadimin Tinubu, Tunde Rahmon ya karyata jita-jitar da ake yi na cewa har an yi masa aiki a Turai, ya ce ‘yan adawa ne suke yada irin karyar nan da suka saba.

Kwanaki an yi rade-radin Tinubu ya mutu

Kwanaki baya ne kafafen sada zumunta su ka cika da jita-jitar cewa Bola Tinubu ya mutu, amma tuni ofishin sa na yada labarai ya karyata wadannan rahotannin.

Bayan jita-jitar, Tinubu mai shekara 69 a Duniya ya dawo daga kasar UAE, ya isa Legas cikin koshin lafiya, ya kunyata wadanda su ke yi masa fatan mutuwa.

Hotunan haduwarsu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel