PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya

PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya

  • Jam'iyyar PDP ta soki ziyarar da shugaba Buhari ya kai zuwa Landon domin duba lafiyarsa
  • PDP ta ce, tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan ba komai bane fa ce lalata dukiyar kasa kawai
  • Ta kuma zargi cewa, shugaban zai iya halartar taron ta yanar gizo maimakon bata kudin kasa

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta soki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan domin duba lafiya da kuma halartar wani taron koli kan fannin ilimi duk dai a Landan din, jaridar Punch ta ruwaito.

PDP ta ce, tafiyar shugaban ba komai bane face son amfani da albarkatun kasa don halartar taro wanda zai iya halartar ta yanar gizo; kamar yadda wadanda suka shirya taron suka tsara.

PDP ta kuma yi Allah wadai da Fadar Shugaban Kasa kan kokarin boye ganawarsa ta sirri da likitocinsa a karkashin taron da zai halarta, tare da yin tir da rashin cika alkawuran shugaba Buhari na zaben 2015 cewa ba zai je kasar waje domin duba likita ba.

Kara karanta wannan

Zan iya ziyartar Daura duk makonni biyu kuma babu wanda zai iya hana ni, Buhari

Tafiyar Buhari zuwa Landan yaudara ce, ba tafiyar duba lafiya bace, in ji PDP
Tutar jam'iyyar PDP | Hoto: premiumtimesng.com

Jam’iyyar adawar ta fitar da sanarwar ne a ranar Talata 27 ga watan Yuli, ta hannun Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Kola Ologbondiyan, mai taken, ‘PDP Lampoons Buhari for Travelling to London for Virtual Meeting.’

Sanarwar ta karanto cewa:

“Jam’iyyar ta dage cewa Shugaba Buhari ba shi da wata hujja ta zuwa nisan duniya Landan tunda ganawar ta yanar gizo ce, ko don a duba lafiyarsa, wanda da zai iya yi a gida da gwamnatinsa ba ta lalata tsarin kiwon lafiyarmu ba.

Wani yankin sanarwar ya caccaki shugaba Buhari, tare da zarginsa da almubazzaranci da dukiyar kasa akan karan kansa yayin da al'ummar kasa ke mutuwa bisa mummunan tsarin kiwon lafiya.

Hakazalika, ta kuma yi tir da halartar taron na fannin ilimi, tare da koka wa kan halin da dalibai ke ciki a Najeriya da cewa, halartar ba zai amfanar da komai ba kasancewar babu tsaro balle dalibai su je makaranta saboda gangancin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiya Ta Shawarci Sunday Igboho Da Nnamdi Kanu Su Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa

Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Landan, kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa da kuma halartan taron kasa da kasa kan inganta ilimi a duniya.

Buhari ya isa Ingila da cikin dare a jirgin shugaban kasa Eagle001.

Ya samu kyakkyawan tarba daga Jakadan Najeriya dake Landan, Amb. Sarafa Ishola, da shugabar yankin Sussex, Mrs Jennifer Tolhurst, da kuma Mr David Pearey.

Fadar shugaban kasa ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki da safiyar Talata, 27 ga Yuli, 2021.

Wata sabuwa: Kwararrun likitocin Najeriya za su tsunduma yajin aiki

A wani labarin, Kungiyar Kwarrarun Likitoci ta MDCAN a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki na sai baba ya gani kan wata bukata da ta ke dashi na gyara tsarin albashin mambobinta, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban MDCAN na kasa, Farfesa Keneth Ozoilo, ya ba da wa’adin kwanaki 21 na shiga yajin aiki a taron manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato, ranar Litinin, 26 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'an Jamhuriyar Benin na yi wa Sunday Igboho da matarsa ‘yar kasar Jamus tambayoyi

Ya ce an yanke shawarar bayar da wa'adin ne yayin taron gaggawa na kungiyar ta kasa da aka gudanar a ranar 19 ga Yulin 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel