Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Shehu Shagari
- Daga Landan, Buhari ya aiko da sakon ta'azziyarsa da iyalan Shagari
- Wannan ya biyo bayan rasuwar maidakin marigayin
- An yi jana'izarta a Masallacin tarayya dake Abuja
Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan tsohon shugaban kasa, Marigayi Alhaji Shehu Shagari, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Hadiza Shagari.
Buhari ya siffanta uwargidar a matsayin babbar wacce ta rike iyalin tun bayan rasuwar maigidanta wanda ya yiwa kasar nan bauta.
Ya aika sakonsa hga gwamnati da al'ummar jihar Sokoto.
Shugaban kasan ya yi addu'an Allah ya yafe mata kura-kuranta kuma ya azurtata da Aljannah.
Hadiza Shagari ta mutu bayan fama da cutar korona
Mun kawo muku rahoton cewa Allah ya yi wa Hadiza Shagari, matar marigayi tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari rasuwa, tana da shekaru 80 a duniya.
Wata sanarwa da ‘dan tsohon shugaban kasar, Bala Shagari ya fitar, ya bayyana cewa ta mutu ne sakamakon cutar korona a cibiyar killace masu cutar da ke Gwagwalada.
A yi jana’izarta a yau Alhamis, 12 ga watan Agusta, bayan sallar la’asar a babban masallacin kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng