Batun sace kwamishinan Neja: Gwamnati ba za ta tattauna da miyagu ko biyansu fansa ba
- Gwamnatin jihar Neja ta sake jaddada matsayarta kan batun tattaunawa da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane
- Gwamnati ta ce tana kan bakanta, kuma ba za ta taba zama da 'yan ta'adda masu cutar da al'umma ba
- Batun ya biyo bayan gano yadda iyalan wani kwamishina ke tattaunawa da 'yan bindigan da suka sace kwamishinan
Niger - Iyalan kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Alhaji Mohammed Sani Idris, sun fara tattaunawa da wadanda suka sace kwamishinan, gwamnatin jihar ta ce.
Gwamnati ta kuma tabbatar da cewa wadanda suka sace kwamishinan sun tuntubi dangin inda a lokacin suka nemi N500m.
Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya fada wa THISDAY a wata hira ta wayar tarho jiya Laraba 11 ga watan Agusta cewa dangin ba za su iya biyan irin wadannan makudan kudaden da ake nema ba, “don haka suna tattaunawa da masu garkuwa da mutanen.”
SSG ya ce masu garkuwar ba su tuntubi gwamnatin jihar ba, inda ya nuna cewa “gwamnati ba ta tattaunawa da 'yan bindiga ko masu garkuwa da mutane.”
Sai dai, a bangare guda SSG ya yi bayanin cewa gwamnati tana daukar matakai don tabbatar da cewa an ceto kwamishinan da aka sace, amma ya ki bayyana matakan da aka riga aka dauka saboda "dalilai na tsaro."
Da aka tambaye shi ko gwamnatin jihar tana sane da inda ake tsare da Idris, ya ki cewa komai game da batun, saboda tsaro.
Wane hali kwamishinan ke ciki a yanzu?
Duk da haka, bincike mai zaman kansa ya nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun kira iyalan kwamishinan a jiya Laraba inda aka tabbatar musu cewa yana cikin koshin lafiya.
An yi garkuwa da Idris ne daga gidansa da ke cikin garin Babantunga a karamar hukumar Tafa da misalin karfe 11 na dare a ranar Lahadin da ta gabata ne yayin da wasu mutane dauke da makamai suka afka masa.
Wadanda suka sace Kwamishina a Neja sun bukaci 'yanunuwa su hada masu Naira Miliyan 500
Miyagun da suka tsare kwamishinan harkokin yada labarai na jihar Neja, sun tuntubi ‘yanuwansa, sun bukaci a biya kudin fansa.
Jaridar The Nation ta ce ‘yan bindigan da su ka yi garkuwa da Malam Sani Mohammed Idris, sun fada wa iyalinsa su kawo Naira miliyan 500.
Rahoton da aka fitar a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021, ya ce miyagun ‘yan bindigan sun ce sai an biya kudin sannan kwamishinan zai fito.
Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai
A wani labarin, Kungiyar Daliban Najeriya ta kasa (NANS) ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana barayin da ke sace dalibai a yankin arewacin kasar a matsayin ‘yan ta’adda.
Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya yi wannan kiran ne a madadin kungiyar a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, a Ado-Ekiti, jihar Ekiti.
Legit.ng ta tattaro cewa Asefon ya ce duk wanda ke da halin yin garkuwa da kashe dalibai to a bayyana shi a matsayin dan ta'adda kawai.
Ya yi Allah wadai da rufe wasu makarantu a wasu sassan arewacin kasar saboda karuwar satar dalibai, Nigerian Tribune ta kuma bayyana.
Asali: Legit.ng