Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan shirin sakin manyan kwararrun masu hada bama-bamai na Boko Haram
- An yi watsi da rahotannin cewa rundunar sojin Najeriya na niyan sakin akalla ‘yan ta’addan Boko Haram biyu da ke hannunta
- Mai magana da yawun NA, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ne ya yi wannan raddi, a ranar Talata, 10 ga watan Agusta
- Nwachukwu ya yi bayanin cewa rundunar, ta hanyar Operation Safe Corridor, na shirin gyara maharan tare da tura su ga hukumomin da suka dace daga bisani
Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da martani game da ikirarin karya da ke cewa tana shirin sakin wasu kwararrun yan Boko Haram guda biyu wadanda a halin yanzu ake yi masu gyara.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na Facebook, mai magana da yawun NA, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya lura cewa mutanen da ke yada irin wannan karairayi suna yi ne da gangan don cimma munanan manufofi.
A wani yunƙuri na daidaita gaskiyar lamari, Nwachukwu ya ce a matsayinsu na ƙwararrun hukuma, rundunar ta yanke shawarar cewa "za a karɓi duk 'yan ta'adda da suka mika wuya, a sarrafa su, sannan a mika su ga hukumomin da suka dace na gwamnati don ci gaba da kulawa daidai da manyan tanade -tanade."
Ya yi bayanin cewa Operation Safe Corridor da ke gudana, wanda ke kula da aikin gyaran, hukuma ce da gwamnatin tarayya ta kafa ba NA ba kuma don haka, kuskure ne a yanke cewa rundunar za ta 'yantar da 'yan ta'addan da suka tuba.
Kakakin ya bayyana cewa Sojojin Najeriya ba za su taba yin hakuri ba, karfafawa, ko shiga cikin duk wani aiki na rashin bin doka kamar kisan gilla.
Matasan mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga
A baya mun kawo cewa akalla mutum 45 wanda ya hada da mayakan Boko Haram/ISWAP matasa yan kasa da shekaru ashirin guda 14 tare da mata da yara 31 sun mika wuya ga Sojoji a ranar Litinin.
An tattaro cewa tubabbun yan ta'addan sun alanta fitarsu daga Boko Haram ne a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng