Dan Najeriya na shirin angwancewa da kyawawan mata biyu a lokaci guda

Dan Najeriya na shirin angwancewa da kyawawan mata biyu a lokaci guda

  • Wani dan Najeriya ya sa mutane da dama tofa albarkacin bakunansu a kafafen sada zumunta yayin da zai angwance da kyawawan mata biyu a lokaci guda
  • Wani mutum da ya yi ikirarin cewa shi abokin ango ne ya wallafa kwafin katin gayyatar daurin auren nasu a shafin Facebook
  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun nuna mamakin wannan ci gaba inda wasu suka ce da alama mazan aure sun fara tsada

Jihar Delta - Wani dan Najeriya na shirin angwancewa da mata biyu a rana daya.

Emmanuel Gwatama wanda aka ce abokin angon ne shine ya wallafa hoton katin gayyatar auren mutumin a Facebook.

Dan Najeriya na shirin angwancewa da kyawawan mata biyu a lokaci guda
Za a daura auren ne a jihar Delta Hoto: Facebook/Emmanuel Gwatana, shutterstock
Asali: UGC

Da yake bayyana Kome a matsayin gwarzon shekara, Emmanuel ya bukaci abokansa na Facebook da su yi shirin halartar bikin auren.

Matan kamar yadda aka gani a katin daurin auren an bayyana sunayesu a matsayin Maro da Akpove.

An shirya gudanar da auren gargajiya a ranar Lahadi, 15 ga watan Agusta, a gidan marigayi Ekpe Hitler, kusa da gidan man Ugala, Isoko ta kudu a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Haramun ne: Wani dalibi ya gina gunkin Aisha Yesufu, aikinsa ya jawo cece-kuce

Da yake wallafa kwafin katin daurin auren a kungiyar Facebook na Igbo Rant HQ, wani mutum mai suna Iyke ya yi tambaya:

"Matan gidan nan shin za ku yarda da wannan yanzu da maza suka yi ƙaranci?"

Jama’a sun yi martani a shafin soshiyal midiya

Okuneye Dare Ifeanyi ya rubuta:

"Da zaran ka ga sunan wajen taron bikin .... tabbas za ka fahimci cewa mata 2 ba za su isa ba."

Miracle Ralu yayi sharhi:

"Sun yi kama da tagwaye kun san wasu tagwaye da rigimarsu! Maza sun yi karanci fa! Tambayi mazan da ke neman matan aure yadda ake ciki za ku fahimci halin da ake ciki."

Chibuike Chibuike ya ce:

“Babu mamaki daya ta kasance tare da shi a lokacin da bai da kudi sannan dayar kuma ta mayar dashi wani a rayuwa, kila shine yasa zai auresu su duka.”

Fasto ya maka jikansa a kotu bayan yayi wuff da zukekiyar matarsa

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

A wani labarin, babban faston wata coci dake Makurdi, jihar Benue ya maka jikansa a kotu bisa zarginsa da kwace masa matarsa da dansa.

Fasto Sale Ekah, mai shekaru 73 ya mika karar ne a babbar kotun yanki dake Makurdi jihar Benue inda yace yana so a kwatar masa hakkinsa akan wannan kwacen mata mai juna biyu da jikansa yayi masa har sai da ta haifi da namiji a wurinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel