Haramun ne: Wani dalibi ya gina gunkin Aisha Yesufu, aikinsa ya jawo cece-kuce
- Gunkin Aisha Yesufu da wani matashi ya gina ya jawo cece-kuce yayin da aka yi ta tofa albarkacin baki
- Wasu sun yaba tare da nuna dama Aisha Yesufu ta cancanci hakan saboda gwagwarmaryar da ta ke yi
- Wasu kuwa sun nuna kyamar hakan saboda a cewarsu, addinin Islama ya haramta gina gunkin mutum
Wani matashi dalibi dan Najeriya mai suna Omoregie Emmanuel ya gina gunkin 'yar gwagwarmaya kuma 'yar kasuwa Aisha Yesufu.
Dandalin Just Event Online ta ba da rahoton cewa Omoregie ya gina gunkin a matsayin wani bangare na ayyukansa don kammala karatun digiri a fannin fasahar zane-zane na 'Fine and Applied Arts'.
Saurayin ya zabi ya gina gunkin A'isha ne domin yaba mata bisa gwagwarmayar da ta yi a 'yan kwanakin nan. Omoregie ya kaddamar da aikin gunkin a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta.
A cikin hotunan da aka yada a kafafen sada zumunta, gunkin ya nuna shahararren hoton Aisha yayin da take daga tutar Najeriya a sama.
Jama'a sun yi ca wajen cece-kuce kan gunkin
Mutane da dama sun yi sharhi kan wannan gunki da matashi ya gina. Wasu na yabawa wasu kuwa na fadin hakan bai dace ba, tare da bayyana dalilansu
Awodeji Oluremi ya ce:
"Wannan abin a yaba ne, ina taya Aisha murna."
Yahaya Mohammed yayi sharhi, ya ce:
"Wannan ba al'adar Islama bane, haramun ne!"
Waheed Qodir ya rubuta:
"Ta cancanci hakan."
Khadeejat AbdulGaniy Olabisi ta ce:
"Gunki haramun ne a Musulunci."
Kalli hotunan:
Yadda masu tattara shara suka dawowa da tsohuwa N10,287,000 da ta zuba a shara
A wani labarin, Wasu dangi a kasar Amurka, Ohio, an ce sun zubar da tsabar kudi $25,000 (N10,287,000) cikin kuskure lokacin da suke taimaka wa kakarsu a aikin tsaftace gida.
Wannan ya faru ne a gundumar Lorain in ji rahoto. An ce dangin sun ci sa’a, wani kamfanin tattara shara ya yi nasarar lalubo shara sannan ya kwaso kudin bayan zubar da kunshin kudin. A cewar ABC News 5, tuni aka mika kudin ga tsohuwa mai kudin.
A cewar Ohio Insider, mai kula da ayyukan tattara sharan, Gary Capan ya ce tawagarsa ta taimaka wa dangin da ba a ambaci sunansu ba wajen gano kudin tsohuwar.
Asali: Legit.ng