Fasto ya maka jikansa a kotu bayan yayi wuff da zukekiyar matarsa

Fasto ya maka jikansa a kotu bayan yayi wuff da zukekiyar matarsa

  • Wani babban faston coci dake zargin jikansa da kwace masa mata da 'da ya maka shi a kotu
  • Sale Ekah, faston mai shekaru 73 ya kai karar ne wata kotun yanki dake Makurdi, jihar Benue
  • Ya bukaci kotu da ta yankewa jikansa hukuncin kwartanci, wanda kowa ya san babban laifi ne

Makurdi, Benue - Babban faston wata coci dake Makurdi, jihar Benue ya maka jikansa a kotu bisa zarginsa da kwace masa matarsa da dansa.

Fasto Sale Ekah, mai shekaru 73 ya mika karar ne a babbar kotun yanki dake Makurdi jihar Benue inda yace yana so a kwatar masa hakkinsa akan wannan kwacen mata mai juna biyu da jikansa yayi masa har sai da ta haifi da namiji a wurinsa.

Fasto ya maka jikansa a kotu bayan yayi wuff da zukekiyar matarsa
Fasto ya maka jikansa a kotu bayan yayi wuff da zukekiyar matarsa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Me faston ya shaidawa kotu?

Kamar yadda tsohon ya shaidawa kotu:

Tabbas jikana ne wanda ya kwace min matata. A shekarun baya tana kawo min tallan koko ne sai kuma ta fara zuwa tana taimakamin da ayyuka sakamakon tsufata da ta gani da amincewar iyayenta.

Bayan wani lokaci ta fara nuna alamun tana son aurena amma na nuna mata cewa nayi mata tsufa. Duk da haka ta jajirce ta nace lallai sai na aureta.

Kamar yadda Aminiya Daily Trust ta wallafa, ya kara da cewa:

A ranar wata Alhamis aka daura mana aure bisa al’adar kabilar Idoma kuma sai da na cika duk wasu sharuddan aure.

Jikana ya kwace matata, hakan kwartanci ne

Ya kara da bayyana yadda jikan nasa ya kwace masa mata a 2017, wanda shima dan kabilar Idoma ne kuma ya take dokokin shari’a.

A cewar tsohon, kwartanci yana da hukunci mai tsanani a karkashin kundin manyan laifukan al’adun Idoma, shashi na 387 ya hau kan jikansa.

Jikan nasa mazaunin garin Obagaji ne dake karkashin karamar hukumar Agatu ta jihar, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

Bayan sauraron korafin tsohon daki-daki, alkalin kotun, Mis Rose Loryshe, ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Satumban 2021 domin a gabatar da wanda ake tuhuma kuma ya amsa tambayoyi.

FG zata dage dokar haramta Twitter, za a kafa ofishin Twitter a Najeriya

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa nan babu dadewa gwamnatin tarayya zata dage dokar haramta Twitter da tayi a Najeriya.

Mohammed ya sanar da hakan ne bayan taron majalisar zartarwa ta kasa da suka yi ta yanar gizo wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A yayin bada bayanin sasancin gwamnati da Twitter, kamar yadda The Nation ta ruwaito, minsitan yace tuni Twitter ta amince da kusan dukkan sharuddan da Najeriya ta saka mata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel