2023: Gwamnan APC na arewa ya kai takararsa na shugaban kasa zuwa kudu maso kudu
- Kudirin Gwamna Yahaya Bello na karbar mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da samun karbuwa
- Bello wanda ya kuduri aniyar kawo canji mai kyau a Najeriya ya kaddamar da shirin tallafi a jihar Cross River
- Gwamnan a baya ya bayyana cewa yana son ayyana aniyarsa na shiga takara a zaben shugaban kasa na 2023
Cross River - A kokarinsa na son zama shugaban kasa a 2023, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya kai kudirinsa na takarar shugaban kasa zuwa jihar Cross River.
Vanguard ta rahoto cewa Bello a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta ya kaddamar da wani shiri na tallafawa a jihar ta kudu maso kudu.

Asali: Facebook
Bello wanda ya sami wakilcin Ahmed Mohammed, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, ya sanar da Mike Odey da Zack Odioko a matsayin shugaba da mataimakin jagoran kungiyar tallafin.
Gwamnan ya kuma bayyana Prince Charles Nwaca a matsayin mai kula da kungiyar shiyyar kudu maso kudu.
Mohammed yayin da yake bayyana cewa Bello ya kuduri aniyar kawo canji mai kyau a Najeriya ya yi kira ga masu sauraro cewa halin da kasar ke ciki na bukatar wanda ke da hangen nesa da kuzari don kawo canji a rayuwar talakawan kasa.
Ya ce burin matashin gwamnan na zama shugaban kasa a Najeriya ya samu karbuwa a Cross River.
Takarar Yahaya Bello a 2023: Masu ruwa da tsaki a APC Nasarawa sun sha alwashin yin magana da murya daya
A gefe guda, akakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Rt Hon Ibrahim Balarabe Abdullahi ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki a jihar za su hadu don daukar matsaya daya wajen zabar dan takarar shugaban kasa na 2023.
Abdullahi ya bayyana hakan ne a ranar Talata a zauren majalisar dokokin jihar Nasarawa lokacin da Rt Hon Mathew Kolawole, Kakakin Majalisar Jihar Kogi, ya jagoranci sauran membobin majalisarsa kan takarar Shugaban kasa da Gwamna Yahaya Bello ke yi a 2023.

Kara karanta wannan
2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa
Abdullahi ya ce 'yan jam'iyyar APC na majalisar dokokin jihar Nasarawa suna da kwarin gwiwa kan karfin Gwamna Bello na zama Shugaban Najeriya na gaba a 2023.
Asali: Legit.ng