Takarar Yahaya Bello a 2023: Masu ruwa da tsaki a APC Nasarawa sun sha alwashin yin magana da murya daya

Takarar Yahaya Bello a 2023: Masu ruwa da tsaki a APC Nasarawa sun sha alwashin yin magana da murya daya

  • Za a samu maslaha a jihar Nasarawa idan aka zo zaben dan takarar shugaban kasa na APC a cewar wani dan majalisar jihar
  • Balarabe Abdullahi, kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa ya fadi hakan yayin ziyarar da masu zawarcin takarar Yahaya Bello suka kai masa
  • Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi tare da sauran mambobi sun ziyarci takwaran su na Nasarawa don neman takarar Yahaya Bello

Nasarawa - Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Rt Hon Ibrahim Balarabe Abdullahi ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki a jihar za su hadu don daukar matsaya daya wajen zabar dan takarar shugaban kasa na 2023.

Abdullahi ya bayyana hakan ne a ranar Talata a zauren majalisar dokokin jihar Nasarawa lokacin da Rt Hon Mathew Kolawole, Kakakin Majalisar Jihar Kogi, ya jagoranci sauran membobin majalisarsa don kai masu ziyara game da neman takarar Shugaban kasa da Gwamna Yahaya Bello ke yi a 2023.

Kara karanta wannan

Ba ma bukatarka kuma: Yan majalisa na PDP sun nemi Secondus ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar

Takarar Yahaya Bello a 2023: Masu ruwa da tsaki a APC Nasarawa sun sha alwashin yin magana da murya daya
Jiga-jigan jam'iyyar APC a Nasarawa sun ce sun yarda da Yahaya Bello Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Abdullahi ya ce 'yan jam'iyyar APC na majalisar dokokin jihar Nasarawa suna da kwarin gwiwa kan karfin Gwamna Bello na zama Shugaban Najeriya na gaba a 2023.

Ya kara da cewa a koyaushe majalisar tana magana da murya daya kuma za ta gana da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar domin daukar matsaya daya akan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito.

"Mun yarda da karfin Mai Girma Gwamna Yahaya Bello kasancewar shi mutum ne da ba ya wasa da batun rashin tsaro saboda ba za a sami ci gaba ba idan babu tsaro.
“Mun dauki wannan ziyarar a matsayin abun farin ciki. Mu a nan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa koyaushe muna magana da murya ɗaya kuma koyaushe muna tafiya ta hanya ɗaya.
“Muna son tabbatar muku cewa mu a Jihar Nasarawa za mu yi magana da murya daya kan batun shugabancin 2023.
“Muna da shugabannin da muka yi imani da su sosai. Za mu tattauna wannan ra'ayi naku da shugabanninmu don yin magana da murya daya,” 'in ji Kakakin.

Kara karanta wannan

Shugaban Nijar ya yaba da aikin gwamnan Borno Zulum, ya bashi lambar girmamawa

Kakakin majalisar yayi amfani da wannan dama wajen yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan irin ci gaban da ya samu a fadin jihohin tarayya.

Yahaya Bello ne matashin dan takarar da zai iya gyara Najeriya, in ji wani sanatan Kogi

A gefe guda, Sanata Smart Adeyemi (APC – Kogi ta yamma) ya bayyana Yahaya Bello a matsayin dan takarar shugaban kasar Najeriya da ya fi cancanta da gadon shugaba Buhari a zaben 2023, kuma ya daga Najeriya ta fuskar karfin tattalin arzikin duniya.

Sanatan na Kogi ya bayyana gwamnan na Kogi a matsayin gwamna matashi mai dimbin kuzari, da basirar ilimi da sanin makamar aiki tare da tarihi mai kima, ya kara da cewa yana da abin da zai kai kasar nan zuwa tudun na tsira, Daily Sun ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel