2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa

2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa

  • Da alama Bode George bai yarda da yiwuwar Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya ba a 2023
  • Jigon na PDP a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, ya sha alwashin tashi daga zama dan Najeriya idan Tinubu ya zama shugaban kasa
  • George ya kuma ce mutanen da ke goyon bayan tsohon gwamnan na jihar Legas don ya karbi mulki daga hannun Shugaba Buhari suna bukatar kulawar likita

Lagas - Cif Olabode George, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya ce zai tashi daga zama dan Najeriya idan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023.

George wanda ya kasance bako a shirin Arise TV na The Morning Show a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, ya ce shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa bai cancanci zama shugaban Najeriya ba.

2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa
Bode George ya ce mutanen da ke goyon bayan Tinubu don ya karbi mulki daga hannun Shugaba Buhari suna bukatar kulawar likita Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Jigon na PDP ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake mayar da martani kan ikirarin da aka ce tsohon ministan ayyuka Adeseye Ogunlewe yayi na cewa babu wani dan takarar da ya fi dacewa ya jagoranci kasar nan a 2023 fiye da Tinubu.

Kara karanta wannan

Idan zaben 2023 ya zo, Bola Tinubu bai da satifiket da zai nuna ya yi karatu inji Bode George

Mamban na kwamitin amintattu na PDP (BoT) ya ci gaba da bayyana cewa mutanen da ke kokarin ganin tsohon gwamnan jihar Legas ya zama shugaban kasa suna bukatar gwajin lafiya.

George ya kuma zargi jigon na APC da karkatar da albarkatun jihar Legas da amfani da shi wajen hargitsa PDP.

A wani labarin kuma, dubbannin mambobin jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta YPP a jihar Kwara, kamar yadda the nation ta ruwaito.

This day ta rahoto cewa, kungiyar waɗanda suka sauya shekar da ake kira 'Third Force' (KSTF) sun bayyana cewa dalilin rikicin APC yasa suka fice daga cikinta.

Hakanan sabbin mambobin YPP ɗin sun sha alwashin kwace mulki daga hannun APC a jihar a babban zaɓen 2023 dake tafe saboda kusoshin tafiyar O to Ge sun koma YPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng