Cutar Kwalara Na Kara Yaduwa a Fadin Najeriya Yayin da Ta Kashe Sama da Mutum 146 a Jihar Kebbi

Cutar Kwalara Na Kara Yaduwa a Fadin Najeriya Yayin da Ta Kashe Sama da Mutum 146 a Jihar Kebbi

  • Cutar kwalara ta ɓarke a jihar Kebbi, inda aka tabbatar da ta kashe aƙalla mutum 146 a faɗin jihar
  • Shugaban asibitin Sir Yahaya, Aminu Bunza, ya tabbatar da adadin a wata fira ta wayar tarho
  • Gwamnatin jihar ta samar da kayan aiki da kuma magunguna domin yaki da cutar

Kebbi - Akalla mutun 146 sun rasa rayukansu a jihar Kebbi, a cewar wani jami'in lafiya yayin da cutar kwalara da ta ɓarke a Najeriya ta shiga jihar.

Premium times ta ruwaito yadda cutar kwalara wacce take jawo amai da gudawa take kara cin karenta babu babbaka a Najeriya, inda abun yafi muni a yankin arewa maso yamma.

Cutar ta kashe mutun 75 a jihar Katsina zuwa ranar Talata, yayin da ta kashe 30 a Zamfara, 23 a Sokoto da kuma mutum 119 a Kano.

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu
Wata Cuta Na Kara Yaduwa a Fadin Najeriya Yayin da Aka Tabbatar Ta Kashe Mutum 146 a Jihar Kebbi Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kwalara ta shiga jihar Kebbi

A wata hira ta wayar tarho ranar Laraba da safe, Aminu Bunza, Sakataren Asibitin Sir Yahaya dake Kebbi, ya tabbatar da adadin da suka mutu a jihar.

Kara karanta wannan

Cuta Ta Barke a Jihar Katsina Ta Hallaka Akalla Mutum 60 Wasu 1,400 Sun Kamu

Ya bayyana cewa an fara samun mai ɗauke da cutar kwalara a karamar hukumar Sakaba ta jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Bunza yace akwai wasu mutum dubu 2,028 da suka kamu da cutar zuwa ranar Laraba.

Bunza yace:

"An fara samun mai ɗauke da cutar a kauyen Dirin Daji dake karamar hukumar Sakaba, inda zuwa yanzun ta shiga dukkan kananan hukumomi 20 na jihar."

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Shugaban asibitin ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara ɗaukar matakan da ya dace domin dakile yaɗuwar cutar.

Yace:

"Gwamnati ta samar da kayan aiki da magunguna a dukkan kananan hukumominta kuma ta baiwa ma'aikatan lafiya horo domin tabbatar da dakile yaɗuwar cutar har wurin da ba ta je ba."

Bunza ya yi kira ga al'ummar jihar da su tabbatar da tsaftar gidajensu da kuma yankunan da suke rayuwa, sannan su sha ruwa mai tsafta kaɗai.

A wani labarin kuma Dubbannin Mambobin Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar Hamayya YPP

Kara karanta wannan

Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna

Daruruwan mambobin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kwara sun fice daga cikinta zuwa YPP.

Kungiyar KSTF ta bayyana cewa sun yanke wannan hukuncin ne bisa yanayin yadda suka ga ana ware su a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel